Yaki da Ta'addanci: Najeriya Ta Horas da Dubban Sojoji don Gamawa da 'Yan Bindiga

Yaki da Ta'addanci: Najeriya Ta Horas da Dubban Sojoji don Gamawa da 'Yan Bindiga

  • Hafsun sojin kasan Najeriya ya ce an horas da sojoji 14,000 daga cikin sababbin sojoji 28,000 da shugaba Bola Tinubu ya amince a dauka
  • Waidi Shuaibu ya ce rundunar ta kashe 'yan ta'adda da dama da kama masu laifi 1,877 a farmaki daban-daban da suka kai a fadin Najeriya
  • Rundunar ta kara amfani da jiragen sa ido marasa matuka, motocin yaki da aka kera a cikin gida da sauran kayan zamani domin inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Babban hafsun sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa rundunar sojin kasa ta Najeriya ta riga ta horas da sojoji 14,000.

Ya bayyana cewa suna daga cikin sababbin sojoji 28,000 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a dauka domin karfafa yaki da ta'addanci, 'yan bindiga da sauran manyan laifuffuka.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Yadda ake horon sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya da ake ba horo a Zaria. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta wallafa bidiyon da Laftanar Janar Waidi Shaibu ya yi jawabi a Rivers a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

An horas da sojoji 14,000

Waidi Shaibu ya ce sababbin sojojin sun samu horo mai zurfi kan yaki da ta'addanci, yaki da masu tayar da kayar baya da sauran dabarun yaki na zamani kafin a tura su wuraren ayyuka daban-daban a fadin kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugabannin kafafen yada labarai a wajen bikin ranar sojin kasa ta Najeriya ta 2026 da aka gudanar a Port Harcourt, jihar Rivers.

A cewarsa, bayan ya hau mukaminsa, ya duba karfin rundunar tare da gano bukatar kara yawan jami'an soji saboda kalubalen tsaro da ke kara kamari a kasar.

Wuraren da aka horar da sojoji

Shaibu ya ce sojoji 6,000 sun kammala horo a cibiyar horaswa ta Zariya, wasu 5,000 a makarantar horaswa ta Osogbo, yayin da ake sa ran karin sojoji 3,000 za su kammala horo a cibiyar horaswa ta Amasiri-Edda.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta yi magana kan raɗe radin janye sojojin Amurka daga Najeriya

Ya ce rundunar ta sake fasalin tsarin horaswa domin tabbatar da cewa sababbin sojoji sun shirya yadda ya kamata domin fuskantar yaki a zamanance.

A cewarsa, sababbin sojojin na shafe kusan watanni 11 suna samun horo kan harbi, yaki da ta'addanci, yaki da masu tayar da kayar baya da sauran dabarun yaki kafin a tura su aiki.

Waidi Shuaibu a Rivers
Hafsun sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shuaibu a Rivers. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Sojoji na farautar 'yan ta'adda

Babban Hafsan ya kuma ce rundunar ta kara kaimi wajen kai hare-hare kan 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka, inda ta kashe wasu tare da kama mutane 1,877.

Vanguard ta wallafa cewa ya danganta wannan nasara da ingantattun kayan aiki, kyakkyawan horo, hadin gwiwa da kuma goyon bayan gwamnatin tarayya.

An kama dan ta'adda a fada

A wani labarin, mun kawo muku cewa jami'an tsaron Najeriya sun cafke wani mutum da ya nufi fadar sarki da bindiga a Akwa Ibom.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya yi barazanar harbi a fadar kafin a kira jami'an tsaro cikin gaggawa su kama shi tare da kwace makamin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yaba wa jami'an da suka kama shi, tare da kira ga al'umma su cigaba da bayar da hadin kai ga hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng