Tinubu Ya Zabi Jihar da za a Kafa Sabuwar Bataliyar Sojoji a Arewacin Najeriya

Tinubu Ya Zabi Jihar da za a Kafa Sabuwar Bataliyar Sojoji a Arewacin Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara domin karfafa yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da sauran miyagu
  • Sabon sansanin zai kasance a Omu Aran, kuma ana sa ran zai kara yawan dakaru da kayan aikin soji domin inganta tsaro a jihar
  • Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yabawa Tinubu da hafsan soji, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen dakile hare-haren da ake fama da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Kwara - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a jihar Kwara a wani mataki na karfafa tsaro da kuma yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.

Sabon sansanin sojin zai kasance ne a Omu Aran, hedikwatar karamar hukumar Irepodun, kuma ana sa ran zai kara yawan dakaru da kayan aikin soji domin inganta ayyukan tsaro a yankunan da ke fama da hare-haren miyagu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Shugaba Bola Tinubu ya amince a kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da yake ganawa da shugabannin rundunonin soja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Gwamnan Kwara ya yabawa Tinubu

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakin Babban Sakataren Yada Labaransa, Mashood Agboola, ya fitar ranar Talata, in ji rahoton Daily Trust.

Ya ce amincewar shugaban kasa ta sake nuna kudirin gwamnatin tarayya na magance matsalolin tsaro a jihar.

AbdulRazaq ya gode wa Tinubu bisa amincewa da kafa sabon sansanin, yana mai cewa hakan zai kara karfin ayyukan dakile ta'addanci da kuma yaki da masu garkuwa da mutane.

A cewarsa, ya kuma yaba wa Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, saboda gaggawar da ya yi wajen aiwatar da bukatar da gwamnatin jihar ta gabatar.

Godiya ga hukumomin tsaro

Gwamnan ya kuma yabawa Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro da sauran hukumomin tsaro saboda kokarinsu na dakile laifuffuka a jihar.

Ya ce hukumomin na gudanar da ayyuka daban-daban domin kawo karshen garkuwa da mutane, ceto wadanda aka sace da kuma fatattakar miyagu daga dazukan jihar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Matsalar tsaro ta kara tsananta

Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar, musamman a garin Babanla da ke karamar hukumar Ifelodun.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya jinjinawa Tinubu kan kafa bataliyar sojoji a Kwara.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya na jawabi a Ilorin. Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mazauna yankin sun yi ikirarin cewa ’yan bindiga na ci gaba da gudanar da hare-hare cikin sauki duk da matakan tsaro da ake dauka.

Rahotanni sun ce a harin da aka kai ranar Litinin, wasu dauke da makamai sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wani, lamarin da ya kara tayar da hankalin mazauna yankin.

Wasu daga cikin mazauna sun kuma yi zargin cewa akwai masu fada a ji da ke hana su bayyana halin da suke ciki a fili, duk da ci gaba da hare-haren da ake kai musu.

Sojoji sun kara kaimi a Kwara

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da manyan hare-hare a jihohin Kwara da Niger domin kakkabe 'yan bindiga da masu garkuwa.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Mutanen gari sun aika sako ga Tinubu kan hare haren 'yan bindiga

Birgediya Janar Nicholas Rume ya bayyana cewa an kafa sababbin sansanonin soja a Patigi da Ilemona domin tabbatar da tsaro.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya jinjina wa sojoji wajen dawo da zaman lafiya tare da alkawarin cigaba da ba su goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com