Hadiza Sabuwa da Sauran Mata da Aka Rantsar a Kujerar Mataimakan Gwamnoni

Hadiza Sabuwa da Sauran Mata da Aka Rantsar a Kujerar Mataimakan Gwamnoni

  • Akwai matan da suka shiga takarar Mataimakan Gwamna a jihohi 15, shida a ciki sun lashe zabensu
  • Bayan shekaru hudu a ofis, za a sake rantsar da Hadiza Sabuwa Balarabe tare da Uba Sani a Kaduna
  • Akon Eyakenyi ta ci zabe a PDP, Noimot Oyedele da Patricia Obila suka yi nasara a Jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - A siyasar Najeriya, an fara samun mata su na rike manyan mukamai, har ta kai su na zama mataimaka ko su nemi takarar Gwamna a jihohi.

Daily Trust a wani rahoto, ta kawo matan da za su zama na biyu a jihohinsu. Abin ya kai an taba yin wata mace da ta hau kujerar Gwamna a Anambra.

Daga cikin mata 24 da suka yi takarar mataimakan Gwamnoni a jihohi 15 na kasar nan a zaben da ya wuce, an yi dace shida daga ciki sun yi nasara.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

Daga yankin Arewacin Najeriya, mata za su rike mataimakan gwamnoni a jihohi biyu – Kaduna da Filato. Daga kudu kuma za ayi haka a jihohi hudu.

A lokacin da ake tunawa da mata a duniya, mun kakkabe wannan rahoto.

Ga jerin matar nan kamar yadda rahoton ya kawo:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Dr Hadiza Balarabe Sabuwa (Kaduna)

Tun 2019 Hadiza Sabuwa Balarabe ta zama mataimakiyar Gwamna Nasir El-Rufai. Likitar da ta shiga siyasa ta canji Marigayi Bala Bantex da ya tafi takarar Sanata.

Hadiza Sabuwa Balarabe ta fito ne daga garin Sanga, ta rike PHCDA kafin shiga takarar 2019. ‘Yar siyasar za ta zarce a wannan kujera tare da Sanata Uba Sani.

2. Josephine Piyo (Filato)

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 Misis Josephine Piyo za ta shiga ofis a matsayin mataimakiyar Gwamnan Filato bayan nasarar da suka samu a inuwar PDP.

Kara karanta wannan

Sace ƴan firamare: An gano yawan daliban da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Piyo ta yi fice a siyasar jihar Filato, ta taba zama shugaban karamar hukumar Riyom, sannan ta je majalisar dokoki kafin zama abokiyar takarar Caleb Mutfwang.

3. Dr Akon Eyakenyi (Akwa Ibom)

Daya daga cikin matan da suka lashe zaben Gwamna a yankin Kudu maso Kudu ita ce Dr. Akon Etim Eyakenyi mai jiran gado a jihar Akwa Ibom a karkashin PDP.

Hadiza Sabuwa
Dr. Hadiza Sabuwa da Uba Sani Hoto: @UbaSaniUs
Asali: Facebook

Yanzu haka Akon Eyakenyi Sanata ce a majalisa. Gwamna Obong Victor Attah ya fara ba ta Kwamishina a 2000 kafin ta zama Ministar Goodluck Jonathan.

4. Dr Ngozi Nma Odu (Rivers)

Dr. Ngozi Nma Odu wanda Farfesa ce a Jami’ar PAMO ta Fatakawal ta na cikin matan da aka rantsar a kujerar mataimakan Gwamna a karshen Mayun 2023.

Ba wannan ne karon farko da mace za ta hau wannan kujera a Ribas ba. Bayan aiki da NLNG, UNDP, da Total, Odu ta rike sakatariyar din-din-din a gwamnatin jiha.

5. Noimot Salako Oyedele (Ogun)

Kara karanta wannan

Matasa da mata sun ɓarke da zanga-zanga kan yunƙurin majalisa na tsige mataimakin gwamna

Daga kudu maso yamma, Injiniya Noimot Salako-Oyedele za ta zarce a kan kujerar mataimakiyar Gwamnan Ogun. Tun 2019, ita ce takawarar Christianah Afuye.

‘Yar siyasar Injiniya ce wanda tayi karatun zamani a garuruwan Legas da Landan. 'Yar siyasar mai shekara 58 a duniya tana auren Kashif Bode Oyedele.

6. Patricia Obila (Ebonyi)

Idan aka koma Kudu maso gabas, akwai Patricia Obila wanda ta lashe zaben Gwamnan Ebonyi tare da Hon Francis Ogbonnaya Nwifuru a jam’iyyar APC mai-ci.

A baya Honarabul Patricia Obila ta rike shugabar karamar hukumar Afikpo ta Arewa sau biyu.

Shugabancin PDP a Najeriya

Ku na da labari cewa tsakanin 1999 da 2005, Olusegun Obasanjo ya yi fada da Solomon Lar, Barnabas Gemade da Dr. Audu Ogbeh a jam'iyyar PDP.

Haka zalika Vincent Ogbulafor ya rasa kujerarsa da ya yi kokarin hana mulki barin Arewa da Umaru ‘Yaradua ya rasu, yanzu an yi waje da lyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari makaranta, sun dauke yaran firamare

Asali: Legit.ng

Online view pixel