'Yar Najeriya Mai Hijabi da Nikabi da Wasu Dalibai Sun Je China Sun Ci Gasar Duniya
- Tawagar Najeriya ta kafa tarihin lashe lambar zinare a rukunin a gasar Spelling Bee ta duniya da aka gudanar a birnin Shanghai na kasar China
- Tawagar da ta kunshi dalibai hudu ta doke sauran kasashen duniya inda daliba Maryam Yusuf mai sanye da nikabi ta sake jan hankalin duniya da kwazonta
- An bayyana cewa wannan ne karon farko da Najeriya ta halarci gasar a matakin duniya, wanda hakan ya jawo farin ciki da alfahari ga 'yan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Shanghai, China – Najeriya ta samu gagarumar nasara a fannin ilimi a matakin duniya yayin da tawagar kasar ta lashe lambar zinare a gasar Spelling Bee ta shekarar 2026 a China.
Tawagar Najeriya ta doke dalibai daga kasashe daban-daban don samun kyauta a matsayin ta farko, wanda hakan ya zama tarihi domin shi ne karon farko da kasar ta halarci wannan babbar gasa ta duniya.

Source: Facebook
Makarantar Ar-Raheem da ke jihar Kwara ta wallafa hotunan daliban a shafinta na Facebook bayan kammala fafatawa da abokan karawarsu a kasar China.
Daliban da suka wakilci kasar sune Oluwadamilola Adeolu daga makarantar St. Lawrence Metropolitan College da ke Ado-Ekiti.
Sauran sun hada da Abdurrahman Yusuf da Maryam Yusuf daga makarantar Ar-Raheem da ke Ilorin; da kuma Chinedu Okediachi daga makarantar Madonna da ke Asaba.
Yayin da suke sanar da nasarar, masu shirya gasar a Najeriya sun yaba wa daliban sakamakon kwarewa da kyakkyawan bajinta da suka nuna wajen daukaka sunan kasarsu a idon duniya.
Kwarewar Maryam Yusuf
Daga cikin wadanda suka fi fice a gasar har da daliba 'yar shekara 14, Maryam Yusuf, wanda bajintarta ta burge mutane da dama.
Dalibar mai sanye da nikabi ta rigaya ta nuna kwarewarta a gasar ta nahiyar Afrika da aka yi a Harare na kasar Zimbabwe, inda ta fafata a matakin manya duk da tana aji uku na karamar sakandare.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali: Girgizar kasa mai girma ta afku a Jamhuriyar Musulunci ta Iran
A gasar ta Zimbabwe, ta yi shiftar kalmomi 17 cikin 20 daidai a cikin minti daya kacal yayin fafatawa ta sauri, wanda hakan ya taimaka wa Najeriya samun matsayi na biyu.

Source: Facebook
Wannan sabuwar nasara da aka samu a kasar China ta haifar da murna a fadin Najeriya, inda iyaye, malamai, da mutane a kafofin sada zumunta ke cike da yabo ga daliban saboda kokarin da suka yi.
Malamin addini ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Legas, Sheikh Tijani Gbajabiamila.
Shugaba Tinubu ya kwatanta marigayin a matsayin jagoran da gudunmawarsa ga addini, zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, da ci gaban al'umma ta bar gurbi mai zurfi a jihar Legas da ma kasa baki daya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya tuno cewa dangantakarsa da Imam Gbajabiamila ta fara tun kafin ya zama gwamnan jihar Legas, kuma ya amfana sosai daga shawarwarin da malamin yake ba shi a matsayinsa na jagoran addini.
Asali: Legit.ng
