Jirgin Sama Dauke da Fasinjoji 68 Ya Gamu da Hatsari a Najeriya

Jirgin Sama Dauke da Fasinjoji 68 Ya Gamu da Hatsari a Najeriya

  • Fasinjoji 68 sun shiga firgici bayan jirgin Enugu Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Benin a jihar Edo
  • Jirgin saman ya gamu da hatsari ne bayan ya wuce karshen titin saukar jirgi ya shiga wani daji da ke kusa
  • Hukumar NSIB ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan lamarin, inda ta tabbatar da cewa an san inda dukkanin fasinjojin suke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Benin, Edo - Akalla fasinjoji 68 sun tsira daga mutuwa a ranar Alhamis bayan wani jirgin sama na Enugu Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Benin da ke jihar Edo.

Jirgin, mai lambar rajista 5N-ENR, yana aiki ne a kan hanyar Enugu–Benin–Lagos lokacin da lamarin ya faru.

Jirgin Enugu Air ya yi hatsari
Jirgin sama na Enugu Air da ya yi hatsari Hoto: @FL360aero
Source: Twitter

Wata majiya a filin jirgin saman Benin ta shaida wa Leadership cewa jirgin ya wuce karshen titin saukar jirgi bayan sauka, sannan ya shiga wani daji da ke kusa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun birkita kauyen Sokoto da harbi, sun sace sama da mutum 50

Yadda jirgin sama ya gamu da hatsari

Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce jami’an Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) sun mayar da martani cikin gaggawa tare da kwashe dukkan fasinjojin daga jirgin cikin aminci.

“Jirgin ya wuce karshen titin saukar jirgi ya shiga dajin da ke kusa. Jami’an FAAN sun gaggauta daukar mataki tare da kwashe dukkan fasinjojin. Babu wanda ya mutu,” in ji majiyar.

A cikin wata sanarwa a shafin X, kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa an kwashe dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin cikin aminci, ba tare da an samu wanda ya ji rauni ko ya mutu ba.

Kamfanin ya ce: “An tsare jirgin kuma an sanar da hukumomin kula da harkokin jiragen sama da abin da ya faru, kamar yadda ka’idojin da aka gindaya suka tanada. A halin yanzu ana gudanar da tantancewar jirgin da kuma yanayin da lamarin ya faru.”

Lamarin ya shafi zirga-zirgar jirage

Kara karanta wannan

Auren gata: Hisbah ta gano makircin da ake shiryawa, ta aika sakon gargadi

Lamarin ya kawo tsaiko na wani dan lokaci ga ayyukan zirga-zirgar jirage a filin jirgin, yayin da jami’an ceto suka tabbatar da tsaron jirgin tare da fara tantance halin da ake ciki.

Enugu Air ta ce matsalar da ta faru yayin saukar jirgin na iya haifar da sauye-sauye na wani dan lokaci ga wasu jadawalin jirage.

Kamfanin ya kara da cewa za a tuntubi fasinjojin da abin ya shafa kai tsaye tare da ba su tallafin da ya dace.

Kamfanin ya tabbatar wa jama’a cewa tsaron fasinjoji da ma’aikatan jirginsa, da kuma ayyukansa, shi ne babban abin da ya fi ba shi muhimmanci, yana mai cewa yana ba da cikakken hadin kai ga hukumomin kula da harkokin jiragen sama yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Jirgin saman Enugu Air ya gamu da hatsari a Benin
Jirgin saman Enugu Air da ya yi hatsari a Benin Hoto: @FL360aero
Source: Twitter

NSIB za ta binciki lamarin

A halin da ake ciki, Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB) ta ce za ta binciki matsalar da ta shafi wani jirgin Embraer E170 a filin jirgin saman Benin.

NSIB ta ce jirgin, wanda ke aiki a matsayin Flight 4264 mai lambar rajista 5N-ENR daga Lagos (LOS) zuwa Benin (BNI), ya gamu da matsalar ne bayan ya wuce karshen Runway 05 yayin sauka.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Wani uba da ƴarsa sun rasu bayan sun fada rijiya a Kano

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa an tabbatar da inda dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin suke, yayin da ba a samu rahoton wani da ya ji rauni ba.

Mutane sun mutu a hatsarin jirgin sama

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin sama na farar hula ya yi hatsari a gabashin ƙasar Faransa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matukin jirgin da dukkan fasinjoji 10 da ke cikinsa.

Mahukuntan yankin sun tabbatar da cewa mutane 11 ne suka mutu a hatsarin da ya faru a kusa da filin jirgin saman garin Tomblaine.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng