Jirgin Sama Dauke da Mutane Ya Yi Hatsari a Saudiyya, An Rasa Rayuka

Jirgin Sama Dauke da Mutane Ya Yi Hatsari a Saudiyya, An Rasa Rayuka

  • An shiga jimami a kasar Saudiyya bayan jirgin sama mai saukar ungulu na ya gamu da hatsari wanda ya jawo asarar rayukan dukkanin mutanen da ke cikinsa
  • Jirgin saman dai mallakin babban kamfanin mai ne na Saudiyya wato Aramco, kuma ya gamu da hatsarin ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026
  • Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin mummunan hatsarin jirgin saman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Saudiyya - Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya gamu da hatsari a kasar Saudiyya da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Hukumomi sun bayyana cewa hatsarin jirgin ya yi sanadiyyar kashe 'yan ƙasar guda 14, inda suka ƙara da cewa jirgin mallakin babban kamfanin mai na ƙasar ne, wato Aramco.

Jirgin sama ya gamu da hatsari a Saudiyya
Jirgin sama samfurin AW139 irin wanda Saudi Aramco ke amfani da shi Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Tashar Reuters tace kmfanin dillacin labarai na Saudiyya (SPA), yayin da yake ambato wani jami'i a ma'aikatar makamashi, ya ruwaito cewa jirgin ya yi hadari ne a yankin Ras Tanura da ke gabashin ƙasar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane

Jirgin sama na Aramco ya yi hatsari a Saudiyya

Hatsarin jirgin saman ya auku ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

“Hadarin ya yi sanadiyyar rasa rayukan daukacin fasinjoji 14 da ke cikin jirgin, waɗanda duka 'yan ƙasar Saudiyya ne."
“Hukumomin da abun ya shafa sun ƙaddamar da cikakken bincike domin gano abin da ya haifar da hatsarin."

Kamfanin Aramco na da jirage

Tashar Channels tv ta ce kamfanin Aramco ya bayyana cewa yana gudanar da aiki da fiye da jiragen sama 60, ciki har da jiragen masu saukar ungulu da ke hidima ga filayen saukar jiragen sama na musamman fiye da 300 a Saudiyya.

Lamarin da ya sa kamfanin ya kasance ɗaya daga cikin masu manyan ayarin jiragen sama na kamfanoni a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan mummunan hatsari yana zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Gulf masu arziƙin mai ke neman haɓaka tare da ƙara yawan man da suke fitarwa biyo bayan hare-haren ƙasar Iran da kuma rufe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ita ce muhimmiyar hanyar ruwa domin fitar da mai da iskar gas daga yankin.

Kara karanta wannan

'Yaran jagoran 'yan bindigan da suka sace Janar sun sake sabon ta'addanci a Katsina

Jirgin sama na Saudi Aramco ya yi hatsari
Wani jirgin sama na kamfanin Saudi Aramco Hoto: Reza
Source: Getty Images

Masarautar Saudiyya ba ta nuna cewa lamarin yana da wata alaƙa da harin maƙiya ba ko kaɗan.

A lokacin yaƙin Gabas Ta Tsakiya, hare-haren Iran sun farmaki rukunin wuraren samar da makamashi a yankin.

Jirgin yakin Amurka ya yi hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutane takwas bayan wani jirgin yaƙi na rundunar sojojin saman Amurka kirar B-52 ya faɗi nan take bayan tashinsa daga sansanin sojin sama na Edwards da ke Kudancin California.

Mummunan lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:20 na safe agogon yankin yayin da jirgin saman ke gudanar da aikin gwaji na yau da kullum.

Gwamnan California, Gavin Newsom, ya bayyana hatsarin a matsayin abin takaici mai muni tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng