Bodejo: Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Neman Belin Shugaban Miyetti Allah
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo, kan kudi N2bn
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar Bello Bodejo da safarar kudin haram da ya kai dala miliyan 2.63
- Babbar Kotun ta bukaci mai tsaya masa ya kasance mazaunin Abuja kuma ya mallaki kadarar da ta kai N2bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo, kan kudi N2bn.
An bayar da belin ne a ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 yayin da ake ci gaba da shari’ar da ake tuhumarsa da safarar kudin haram da ya kai dala miliyan 2.63.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da belin ne bayan ya yanqqqqke hukunci kan bukatar Bodejo.
Kotu ta bayar da belin Bello Bodejo
Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce laifuffukan da ake tuhumarsa da su na da damar beli, kuma kotun tana da ikon bayar da belin.
Alkalin ya umarci wanda zai tsaya wa wanda ake tuhuma da ya kasance da kudin da ya yi daidai da adadin belin, wato N2bn.
Ya ce dole ne mai tsaya masa ya kasance mazaunin Abuja kuma yana da takardar shaidar biyan haraji ta tsawon shekaru uku.
Justice Ekwo ya kuma umarci mai tsaya masa ya mallaki kadarar fili da ta kai darajar N2bn a Abuja. Ya kara da cewa magatakardar kotun zai tantance takardun mallakar kadarar.
Kotun ta hana Bodejo tafiya
Alkalin ya kuma umarci Bodejo da ya mika fasfo dinsa na kasa da kasa ga magatakardar kotun, tare da hana shi fita daga Najeriya ba tare da izinin kotun ba.
Hakazalika ya dage shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoba 2026 domin fara sauraron karar.
EFCC ta tuhumi Bodejo
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da Bodejo a ranar 9 ga Yuli kan tuhume-tuhume da dama da suka shafi zargin safarar kudin haram da ya kai kusan dala miliyan 2.63.
Shugaban na kungiyar Miyetti Allah ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da hukumar EFCC yi masa, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Bayan gurfanar da shi, lauyan masu gabatar da kara, Wahab Shittu (SAN), ya nemi a sanya ranar fara shari’a tare da rokon kotu ta tsare wanda ake tuhuma a hannun EFCC.

Source: Twitter
Sai dai lauyan Bodejo, Ahmed Raji (SAN), ya shaida wa kotun cewa ya shigar da bukatar beli mai dauke da kwanan wata 30 ga Yunin 2026.
Raji ya ce laifukan da ake zargin wanda yake karewa da su na da damar beli karkashin dokar, sannan ya bukaci kotu ta amince da bukatar.
Sai dai, lauyan hukumar EFCC, Wahab Shittu ya yi adawa da bukatar, inda ya roki kotu ta ki bayar da belin.

Kara karanta wannan
Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya
Miyetti Allah ta nemi a saki Bodejo
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Miyetti Allah Miyetti Allah ta yi kira da a saki shugabanta na kasa, Alhaji Bello Bodejo da aka cafke.
Kungiyar Miyetti Allah ta bukaci shugabannin da ke kula da shari'ar da su tabbatar an yi wa shugabansu adalci kasancewar shi ma dan Najeriya ne.
Asali: Legit.ng

