Kisan Kiristoci: Sanatan Amurka Ya Tona Asirin Wasu Jami'an Gwamnatin Najeriya
- Sanata Ted Cruz na Amurka ya zargi wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya da haɗa baki wajen kisan gilla ga Kiristoci a sassan ƙasar
- Cruz ya cetun daga 2009, an kashe Kiristoci sama da 50,000 tare da ruguza majami'u da makarantu 20,000 saboda tsatsauran ra'ayi
- Amma a hannu daya, ma'aikatar wajen Amurka ta tabbatar da cewa Najeriya na nuna ƙoƙarin gyara wannan lamari ta hanyar ɗaukar matakai hudu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – Sanatan Amurka Ted Cruz, ya zargi wasu jami'an gwamnatin Najeriya da hannu dumu-dumu a "kisan kiyashi" da ake yi wa mabiya addinin Kirista.
Cruz ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026, yayin wani taron kwamitin hulɗa da ƙasashen waje na majalisar dattawan Amurka.

Source: Getty Images
Zargin Sanatan Amurka kan kisan Kiristoci

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari
A cewar Sanatan, Najeriya ce ƙasa mafi hatsari ga Kiristoci a duniya, inda ya bayyana cewa an kashe sama da mutane 50,000 tun shekarar 2009, in ji rahoton The Cable.
Ya ƙara da cewa an ƙone majami'u da makarantu sama da 20,000 kurmus, yayin da jami'an gwamnati a matakin tarayya da na jihohi ke nuna halin ko-in-kula ko kuma ma suna taimaka wa masu wannan kisan.
Sanata Cruz ya tunatar da taron cewa ya gabatar da wani kudurin doka mai taken "Kudurin dokar bin diddigin 'yancin addini a Najeriya na 2025" a watan Oktobar bara.
"Wannan kudurin doka zai sanya takunkumi ga jami'an gwamnatin Najeriya da aka samu da laifin taimaka wa masu tsatsauran ra'ayin addini ko kuma nuna wariya ta hanyar dokokin Shari'a a Arewacin ƙasar."
- Sanata Ted Cruz.
Ya bayyana cewa ya taɓa gana wa da manyan jami'an tsaron Najeriya a bara inda suka yi alkawarin kawo ƙarshen tashin hankalin, amma a cewarsa, har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Ma'aikatar Amurka ta yi martani ga sanata
Sai da kuma, Nick Checker, Shugaban sashen kula da al'amuran Afirka na ma'aikatar wajen Amurka, ya yi martani ga wasu daga cikin maganganun Cruz, in ji rahoton The Tribune.
Checker ya bayyana cewa tun bayan da Shugaba Donald Trump ya mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashe masu barazana ga ƴancin addini (CPC), ƙasar ta fara hobbasa don sauya lamarin.

Source: Twitter
Shugaban sashen ya jero wasu nasarori da ya ce gwamnatin Najeriya ta samu da suka haɗa da:
- Canjin shugabanni a hukumomin tsaron Najeriya.
- Ɗaukar sababbin sojoji guda 50,000 domin ƙarfafa tsaro.
- Tura jami'an tsaron dazuzzuka zuwa yankunan Arewa ta tsakiya domin kare Kiristoci.
- Ƙara ƙaimi wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da ta'addanci a gaban kotu.
Hukumar ma'aikatar wajen Amurka ta bayyana cewa suna maraba da waɗannan matakai na farko da Najeriya ta ɗauka, kuma za su ci gaba da haɗa kai da tawagar tsaron ƙasar da Nuhu Ribadu ke jagoranta domin tabbatar da tsaron kowa ba tare da la'akari da addini ba.
Amurka ta sanya wa wasu takunkumi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta fara daukar matakai kan wasu 'yan Najeriya, wadanda take zargin suna goyon bayan kisan kiyashin da ake wa kiristoci a kasar.
Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin hana biza ga duk mutanen da suka jagoranta, suka ba da izini ko suke goyon bayan tauye ’yancin addini a Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar mai taken “Yaki da Mugayen Hare-haren da ake kaiwa Kiristoci a Najeriya da Duniya."
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
