An Tafka Babban Rashi: Daya daga cikin Manyan Limaman Masallaci Ya Rasu a Kwara
- An shiga jimami bayan rashin babban limami a addinin Musulunci wanda ya bayar da gudummawa sosai
- An ce limamin Shonga, Alhaji Jibril Baba Nnatakun, ya rasu a Kwara, lamarin da ya jawo alhini daga al'ummar Musulmi
- Jagoran siyasar Kwara ta Arewa, Mohammed Baba Ibrahim, ya bayyana marigayin a matsayin malami mai hikima da sadaukarwa ga addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Songa, Kwara - Alhaji Jibril Baba Nnatakun, wanda shi ne babban limamin Shonga da ke karamar hukumar Edu a Kwara, ya rasu.
An tabbatar da cewa marigayin ya rasu a ranar Alhamis, 9 ga Yulin shekarar 2026 da muke ciki.

Source: Original
Daya daga cikin wadanda suka yi ta'aziyya shi ne Mohammed Baba Ibrahim, wanda aka fi sani da MBI wanda ya wallafa a Facebook.
MBI na ɗaya cikin fitattun jagororin siyasa ne daga Kwara ta Arewa wanda ya ba alumma gudummawa.
Ta bakin tawagarsa ta yada labarai, MBI ya aika da sakon ta'aziyya ga Sarkin Shonga, Alhaji Haliru Yahaya Ndanusa, da kungiyar SHEDDU da daukacin al'ummar masarautar Shonga.
MBI ya bayyana marigayi Nnatakun a matsayin malamin addinin Musulunci mai sadaukarwa, wanda ya shafe shekaru yana jagorantar al'umma da koyar da addini cikin hikima da tawali'u.
Ya ce halayen kirki, ilimi da jajircewar marigayin wajen yada koyarwar Musulunci sun sa ya samu girmamawa daga sarakuna da sauran al'ummar Shonga baki daya.
MBI ya bukaci al'ummar Shonga su ci gaba da rayuwa bisa dabi'un ibada, gaskiya da hidima da marigayin ya koyar, domin girmama kyakkyawan tarihinsa.
Ya kara da cewa hikima, tawali'u da jajircewar marigayin wajen yada koyarwar Musulunci sun sa ya samu karbuwa a wajen masu mulki da kuma daukacin al'ummar Masarautar Shonga.
MBI ya roki Allah (SWT) da Ya gafarta wa marigayin, Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa, Majalisar Masarauta da daukacin al'ummar Musulmi na Shonga hakurin jure wannan babban rashi.
Har ila yau, ya bukaci al'ummar masarautar su yi koyi da kyawawan halaye na ibada, tsoron Allah da hidimar al'umma da marigayi Babban Limamin ya nuna a tsawon rayuwarsa.
Wakilin Sadaukin Lafiagi ya tabbatar wa Sarkin Shonga da daukacin al'ummar masarautar cewa yana tare da su a wannan lokaci na alhini, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za su ci gaba da samun karfi daga kyakkyawan tarihi na jagoranci, hadin kai da shiriyar da marigayin ya bari.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwar marigayin ko shekarunsa ba. Mutuwarsa ta jawo alhini daga al'ummar Musulmi, shugabannin gargajiya da fitattun mutane a yankin.
Rahotanni sun ce Shonga tsohuwar yanki ne na al'ummar Nupe ce da ke bakin Kogin Niger.
Babban malamin Musulunci ya rasu a Lagos
Mun ba ku labarin cewa duniyar Musulunci ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar malamin addini a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya.
Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila ya rasu ranar Asabar a asibitin LASUTH, lamarin da ya girgiza al'ummar Musulmi.
Ɗansa Ibikunle Lateef ne ya sanar da rasuwarsa ta shafin Facebook, sannan aka yi jana'izarsa a Iponri Central Mosque bisa koyarwar addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng

