Matasa 9 Sun Rasu a Hanyar Neman Arziki daga Sokoto zuwa Legas

Matasa 9 Sun Rasu a Hanyar Neman Arziki daga Sokoto zuwa Legas

  • Wadansu matasa da suka gaji da halin da su ke ciki sun rasa rayukansu a hanyar zuwa jihar Legas bayan sun baro kauyensu a Sakkwato
  • Matasan su tara daga karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato sun rasu a wani mummunan hatsarin mota yayin tafiya Legas neman aiki
  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo/Shagari, Umar Yusuf Danmaje, ya ce mutuwar matasan babban rashi ne ga iyalai da al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Wasu matasa tara daga karamar hukumar Yabo a jihar Sokoto sun rasa rayukansu bayan sun yi hatsarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Legas domin neman ingantacciyar rayuwa da aikin yi.

Lamarin da ya faru ranar Juma'a 17 ga watan Yuli, 2026 ya jefa al'ummar Yabo cikin jimami, inda ake ci gaba da karbar sakonnin ta'aziyya daga sassa daban daban na jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi abin da zai hana Obi da Atiku buge Tinubu a 2027

Matasan Sakkwato 9 sun rasu
Taswirar jihar Sakkwat da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa 'dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Yabo/Shagari, Umar Yusuf Danmaje, ya bayyana alhininsa kan lamarin.

Ana jimami a jihar Sakkwato

The Sun Nigeria ta kawo labarin cewa a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Sokoto, Umar Yusuf Danmaje ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga jihar.

Ya ce:

"Na samu labarin mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu matasa tara daga karamar hukumar Yabo."

Ya kara da cewa:

"Wannan bala'i babban rashi ne ba ga iyalan mamatan kadai ba, har ma da mazabarmu da jihar Sokoto da kasa baki daya."

Dalilin matasan Sakwato na tafiya Legas

Danmajen ya bayyana cewa matasan sun bar gidajensu da ke jihar Sakkwato da burin samun halal da kuma tallafa wa iyalansu idan sun samu aikin yi a jihar Legas.

A cewarsa:

"Waɗannan matasa ne masu burin gina makoma mai kyau ga kansu da iyalansu. Mutuwarsu yayin neman halal abu ne mai matukar tayar da hankali."

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Ana ci gaba da karban ta'aziyyar matasan Sakkwato da su ka rasu
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato yayin wani taro Hoto: Ahmed Aliyu 2023
Source: Facebook

Dan majalisar ya ce wannan ibtila'i ya sake bayyana irin kalubalen tattalin arziki da matasa ke fuskanta, wanda ke tilasta musu yin doguwar tafiya domin neman aiki.

Danmaje ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan, sarakunan gargajiya, shugabannin al'umma da daukacin mutanen karamar hukumar Yabo.

Ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan, Ya sanya su Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.

Hakazalika, ya bukaci hukumomin da ke kula da hanyoyi su kara daukar matakan rage yawan hadurran mota a manyan titunan Najeriya.

Yan ta'adda sun yi barna a Sakkwato

A baya, mun samu labarin cewa wasu mutane da suka dawo gidajensu daga gudun hijira sun fada hannun 'yan bindiga bayan sun kawo hare-hare a karamar hukumar Tambuwal da ke Sakkwato.

Maharan sun yi awon gaba da mutane tare da kwashe dabbobi bayan sabon harin da suka kai a jihar Sakkwato, inda iyalan da suka rasa matsuguni su ka bukaci gwamnati ta kai masu ɗauki.

An dai kai harin ne yayin da mazauna yankin, waɗanda suka shafe lokaci suna neman mafaka a garin Jabo bayan hare-haren da aka rika kai masu a baya, kuma wannan hari an kai shi ne kwana daya da wani harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng