Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashi: Sheikh Tijani Shehu Ya Rasu
- Duniyar Musulunci ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar malamin addini a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya
- Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila ya rasu ranar Asabar a asibitin LASUTH, lamarin da ya girgiza al'ummar Musulmi
- Ɗansa Ibikunle Lateef ne ya sanar da rasuwarsa ta shafin Facebook, sannan aka yi jana'izarsa a Iponri Central Mosque bisa koyarwar addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - An shiga jimami a jihar Lagos bayan sanar da rasuwar wani fitaccen malamin addinin Musulunci.
Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila, mai rike da sarautar Olori Ratibi na Legas, ya rasu da safiyar Asabar, 18 ga Yulin 2026, a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Legas (LASUTH).

Source: Original
Ɗansa, Ibikunle Lateef, ya tabbatar da rasuwar malamin ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Yadda aka yi jana'izar marigayin a Lagos
Daga bisani an tabbatar da gudanar da jana'izarsa a babban masallacin Iponri bisa tsarin Musulunci wanda al'ummar Musulmi da dama suka halarta.
Olori Ratibi muhimmin matsayi ne na shugabancin addinin Musulunci a Legas, wanda ke kula da ayyukan limamai da masu jagorantar sallah a masallatan yankin.
Rasuwar Sheikh Gbajabiamila ta jefa al'ummar Musulmi ta Legas cikin alhini, domin an san shi a matsayin fitaccen malami kuma jagoran addini mai tasiri.
Mutane da dama sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana alhininsu tare da yi masa addu'ar Allah Ya gafarta masa, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Source: Facebook
Gudunmawar da marigayin ya bayar a rayuwarsa
Adams Mutair Olawale ya bayyana marigayin a matsayin babban malamin Musulunci, mai koyarwa da kira zuwa tafarkin Allah, yana mai cewa iliminsa da hidimarsa sun amfani al'umma.
Haka kuma, Okunmoyinbo Mustapha Oluwayemisi da Prince Moshood Olawale Eletu sun yi addu'ar Allah Ya karɓi ayyukansa na alheri, Ya kuma ba iyalansa da masoyansa juriyar wannan babban rashi.
A wani rahoto makamancin wannan, an kuma sanar da rasuwar Sheikh Abdulkadir Muhammad Kamaldeen Al-Adaby a Ilorin, inda jagororin addini da dama suka tabbatar da mutuwarsa.
Godiya daga iyalan marigayin ga al'umma
Ɗan marigayin ya yi godiya ga dukkan wadanda suka halarci jana'izar, suka kira, suka yi mana addu'a, suka aiko da sakonnin ta'aziyya, da kuma wadanda suka yi niyyar zuwa amma suka kasa saboda wasu dalilai da ba su da iko a kansu.
Ibikunle ya ba mutane hakuri bisa kiran wayar da bai samu damar amsawa ba a jiya, haka kuma, ya nemi afuwar duk wadanda suka halarci shirin jana'izar amma ban samu damar ganawa da su ba saboda yawan jama'ar da suka zo domin jajanta mana.
Ya ce suna matukar godiya gare su, ya gode da suka tsaya tare iyalansu tun daga farkon wannan jarrabawa har zuwa jana'izar.
Malamin Musulunci ya rasu a Bauchi
Mun ba ku labarin cewa an sanar da rasuwar babban malamin Musulunci, Sheikh Dawud Muhammad a jihar Bauchi bayan shafe shekaru yana yi wa addini hidima.

Kara karanta wannan
Iyalan budurwar da aka tsinci gawarta a gidan ministan Tinubu sun kai ƙorafi gaban IGP
Rahotanni sun nuna cewa a yau Laraba, 10 ga Yunin 2026 za a gudanar da jana'izar shi, inda aka bukaci jama'a su hallara domin masa addu'a.
Malamai da dama a fadin Najeriya sun bayyana wasu abubuwa da suka sani game da Sheikh Dawud Muhammad tare da rokon Allah ya ji kan shi.
Asali: Legit.ng

