Sanata Ndume Ya Aika Sakon Gaggawa ga Gwamnati kan Daliban da Aka Sace a Borno
- Sanata Ali Ndume ya ce sabon harin da aka kai makarantar Borno ya nuna bukatar gwamnati ta kara daukar karin matakai kan rashin tsaro
- ‘Yan bindiga sun sace dalibai da malamai a lokacin da ake zana jarrabawar NECO a Lassa, yayin da sojoji suka ceto wasu daga cikinsu
- Ndume ya bukaci jami’an tsaro su kara kokari wajen kubutar da sauran wadanda aka sace tare da dakile hare-haren da ka iya zuwa nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya ce sace daliban da ke rubuta NECO a jihar Borno ya nuna cewa gwamnatin tarayya na bukatar kara kokari wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar.
Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar GDSS, Lassa, da ke karamar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno a ranar Litinin, lokacin da dalibai ke rubuta jarrabawar kammala sakandare ta NECO.

Source: Facebook
An sace dalibai da malamai a lokacin jarrabawa
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar sace wasu dalibai da malamai a makarantar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Bayan faruwar lamarin, dakarun sojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun fara aikin ceto domin kubutar da wadanda aka dauka.
Rundunar sojin ta sanar cewa ta samu nasarar ceto dalibai 10, yayin da ake ci gaba da kokarin gano sauran dalibin da bai samu kubuta ba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Sanata Ndume ya nuna damuwa kan harin
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Ndume ya bayyana harin a matsayin abin takaici, yana mai cewa ya faru ne a lokacin da har yanzu ba a san makomar wasu yaran da aka sace a baya ba.
Ya ce:
“Wannan sabon sace-sacen abin damuwa ne, musamman a lokacin da har yanzu ba mu san halin da yaran Mussa da aka sace a watan da ya gabata suke ciki ba.”
Sanatan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara himma wajen kubutar da daliban da aka sace a hare-haren baya-bayan nan a jihar Borno.
Ya ambaci daliban Mussa Primary da Junior Secondary School, wadanda aka sace a baya, da kuma wasu mutanen da aka dauka a Ngoshe da kan hanyar Buratai zuwa Biu.
A cewarsa, ya kamata jami’an tsaro su tabbatar da dawowar dukkan wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Gwamnati ta tabbatar da tsaro da aiki
Ndume ya ce hanya mafi kyau ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ‘yan ta’adda ba su yi galaba a kan gwamnati da jami’an tsaro ba ita ce a kai farmaki kan maboyarsu.
Ya ce dole ne gwamnati ta nuna cewa alkawuran da take yi kan tsaro suna tafiya tare da aiki a kasa.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro da suka bi sawun maharan tare da ceto wasu daga cikin wadanda aka sace.
An bukaci hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro
Sanatan ya jaddada muhimmancin kara hadin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro domin dakile hare-haren ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.
Ya ce hadin kai tsakanin hukumomi zai taimaka wajen hana sake faruwar irin wadannan hare-hare.
Harin ya zo bayan wani sace-sace a yankin
Sabon harin ya faru ne makonni kadan bayan wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka sace dalibai da dama daga makarantar Mussa Primary da Junior Secondary School da ke yankin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da harin na ranar Litinin, inda ta ce wasu dalibai har yanzu ba a gano su ba.
Ta ce jami’an ‘yan sanda, sojoji, mafarauta da kungiyoyin sa-kai suna ci gaba da binciken yankin domin gano wadanda aka sace.
Asali: Legit.ng


