Da Gaske Gwamnatin Tinubu Ta Karbo Bashin Naira Tiriliyan 80? Minista Ya Yi Martani
- Gwamnatin Tarayya ta musanta cewa ta ciyo bashin Naira tiriliyan 80 a karkashin mulkin Shugaba Tinubu
- Ministan Kudi ya bayyana cewa sauyin lissafi da kuma hada tsoffin basussuka ne suka sa alkaluman suka karu a kan takarda
- Majalisar dattijai ta tattauna da ministan kan lamarin tare da kalubalantar wasu daga cikin shirye-shiryen kasafin kudin bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa alkaluman basussukan kasar nan sun yi yawa a idon jama'a, inda ta jaddada cewa kudaden da aka ciyo a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin shekaru uku da suka gabata ba su kusa da Naira tiriliyan 80 da ake yadawa ba.
Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-tsare na Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Source: Twitter
Bayani kan bashin N80trn
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kudi na majalisar dattijai karkashin jagorancin Sanata Sani Musa daga jihar Neja ta tsakiya, in ji rahoton Vanguard.
Ministan ya bayyana hakan ne domin yi wa 'yan majalisa bayani kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.
Da yake martani ga tambayar da Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi ta tsakiya ya yi game da zargin cewa gwamnatin ta ciyo bashi mai yawa, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta ciyo bashi kusa da adadin da ake fadi ba.
Ya bayyana cewa lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, basussukan da ake bi sun kai kusan Naira tiriliyan 75, amma mutane da yawa suna kwatanta wannan adadin da na yanzu ne ba tare da la'akari da wasu abubuwa ba.
Ya ce sauyin darajar naira da sake lissafin kudaden kasashen waje da ake biya ne ya sa alkaluman suka karu da fiye da tiriliyan 40 a kan takarda, ba wai sabon bashi aka ciyo ba.
Batun kudaden Ways and Means
Ministan ya kara da cewa wani abin da ya sa alkaluman suka karu shi ne mayar da tsoffin basussukan Ways and Means na gwamnatin da ta gabata zuwa cikin kundin bashin hukuma bisa amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa.
Ya bayyana cewa an kara kimanin Naira tiriliyan 33 ta wannan tsari, wanda hakan ba sabon bashi ba ne face sanya tsoffin basussuka a cikin litattafan lissafi na gwamnati.

Source: Twitter
Tsarin ciyo bashi da alhakin gwamnati
Jaridar Punch ta rahoto ministan ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu tana taka tsantsan wajen ciyo bashi, kuma ana amfani da kudaden ne kawai don gina ababen more rayuwa maimakon cin abinci.
Sai dai wasu mambobin kwamitin, musamman babban whip na majalisar dattijai, Sanata Tahir Monguno daga jihar Borno, da Sanata Adamu Aliero, sun nuna damuwarsu kan rashin aiwatar da bangaren manyan ayyuka na kasafin kudin 2026, inda suka ce hakan na iya zama babban abin tashin hankali.
"Ba aibu bane ciwo bashi" - Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Abmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai daina karbo wa Najeriya bashin kudi ba matukar akwai bukatar hakan.
Tinubu ya ce maimakon sukar ciyo bashin da ake yi, kamata ya yi Najeriya ta dage wajen ganin ta biya basussukan da ke kanta.
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da karbo rancen kudi.
Asali: Legit.ng


