Majalisa Za Ta Yi wa Ribadu da Ministar Tinubu Tambayoyi kan Badakalar PFIPC
- Kwamitin Majalisar Wakilai ya gayyaci Nuhu Ribadu domin ya bayyana matakan da ONSA ta dauka bayan korafin da aka kai kan PFIPC
- Majalisar ta bukaci Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana da kanta kan bayanan da ma’aikatarta ta gabatar game da PFIPC
- Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce ba ta taba amincewa da PFIPC ba, kuma ta sanar da ONSA bayan gano kura-kurai a takardun kungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken rikicin da ya dabaibaye hukumar bogi ta PFIPC ya gayyaci Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.
An ce majalisar domin ya bayyana matakan da ofishinsa ya dauka bayan samun rahoton ayyukan kungiyar tun a watan Oktoban shekarar 2025.

Source: Facebook
Minista da Ribadu za su je gaban majalisa
Kwamitin ya kuma nace cewa dole ne Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana da kanta domin yin karin bayani kan batutuwan da suka taso daga bayanan da ma’aikatarta ta gabatar, in ji rahoton Tribune.
Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Dunoma Umar Ahmed, ya shaida wa kwamitin cewa ma’aikatar ta sanar da Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro bayan ta gano kura-kurai a takardun da PFIPC ta gabatar.
Ya ce wani da ya bayyana kansa a matsayin shugaban PFIPC, Prince Adeniyi Adeyemi Matthew, ya tuntubi ma’aikatar sau uku domin neman hadin kai wajen shirya taron zuba jari na duniya a Najeriya.
Sai dai ya ce ma’aikatar ta yi watsi da dukkan bukatun bayan gudanar da bincike kan takardun da aka gabatar.
Ribadu ya ce bai san PFIPC ba
Ahmed ya bayyana cewa ma’aikatar ta rubuta wa ofishin Nuhu Ribadu a ranar 16 ga Oktoba, 2025, domin neman karin bayani kan matsayin Prince Adeyemi.
A cewarsa, ofishin ONSA ya mayar da martani a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, inda ta bayyana cewa binciken da aka gudanar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya nuna cewa ba a san Prince Adeyemi ba a kowace hukuma ta gwamnatin tarayya.
Ya kuma shaida wa ’yan majalisar cewa ma’aikatar ba ta taba shiga wata tattaunawa ko hadin gwiwa da PFIPC ba, ko ta taimaka wajen hada kungiyar da masu zuba jari ko gwamnatocin kasashen waje.
Haka kuma, ya ce babu wata yarjejeniya da PFIPC ta taba kulla da wata kasa ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Waje, cewar rahoton Premium Times.

Source: Twitter
Majalisa ta nemi karin bayani
Da yake mayar da martani, shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya tambayi dalilin da ya sa ba a dauki matakin da ya dace ba bayan ONSA ta tabbatar da cewa PFIPC ba ta da wata alaka da gwamnatin tarayya.
Ya ce kwamitin na son sanin irin matakan da hukumomin tsaro suka dauka bayan samun rahoton da Ma’aikatar Harkokin Waje ta aika musu.
ICPC ta titsiye Gbajabiamila kan PFIPC
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar ICPC ta titsiye Femi Gbajabiamila kan zargin da ake yi game da PFIPC da ake takaddama a kai.
Mai ikirarin shugabantar PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da karɓar N400m domin ya samu shugabancin hukumar.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar ya musanta zarge-zargen tare da shigar da ƙarar N15bn kan Adeniyi.
Asali: Legit.ng


