Tinubu Ya Biya N501bn daga Bashin Lantarki, Ya Kaddamar da Sabon Shirin N729bn
- Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe N501bn wajen biyan wani bangare na bashin kamfanonin samar da wutar lantarki tare da cika alkawuran farko
- Gwamnati ta bayyana cewa kamfanonin samar da lantarki takwas da tashoshin wuta 17 sun amfana da biyan bashin da aka fara aiwatarwa
- Bayan biyan kudin ruwa na farko kan lokaci, gwamnati ta ce yanzu za ta kaddamar da sabon shirin bashin N729bn domin bunkasa bangaren lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta cika dukkan alkawuran da ta dauka a karkashin kashi na farko na shirin biyan bashin bangaren wutar lantarki, inda ta kashe kusan Naira biliyan 501 wajen rage bashin da ake bin ta na tsawon shekaru ga kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos).
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa ta biya kudin ruwa na farko kan jadawalin bashi a kan lokaci, abin da ta ce ya kara karfafa amincewar masu zuba jari da kasuwar lantarkin Najeriya.

Source: Twitter
Tinubu ya fara biyan bashin lantarki
Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin taron masu zuba jari kan sabon shirin bashin NBET Finance Company Plc Series II Bond a Abuja, in ji rahoton Punch.
Ta ce ya zuwa yanzu an biya kusan Naira biliyan 333 ga kamfanonin samar da lantarki takwas da ke gudanar da tashoshin samar da wuta 17.
A cewarta, gwamnatin Tinubu ta zabi ta fara cika alkawuranta ga masu zuba jari kafin sake komawa kasuwar hada-hadar bashi domin neman karin kudade.
Verheijen ta ce gwamnati ba wai ta sake tsara bashin kawai ba, illa tana mayar da tsofaffin basussukan zuwa sabon jari domin bunkasa bangaren lantarki.
Gwamnati ta biya kudin ruwa kan lokaci
Jaridar Vanguard ta ruwaito Verheijen tana cewa a watan Fabrairun shekarar 2026, gwamnatin tarayya ta ware kusan N501bn domin shirin.
A cewarta, daga cikin kudin, N300bn an biya ne kai tsaye, yayin da N201bn aka samar ta hanyar takardun bashi.
Ta kara da cewa wannan ya rufe kusan kashi 22 cikin 100 na bashin da aka amince da biya, yayin da za a ci gaba da biyan sauran bashin ta hanyar sabon shirin Series II da wasu shirye-shiryen da za su biyo baya.
Verheijen ta kuma bayyana cewa gwamnati ta biya kudin ruwa na farko na kusan N63.5bn a ranar 14 ga Yulin 2026, kamar yadda aka tsara.

Source: Twitter
Tinubu ya kawo sabon shirin N729bn
A cewar gwamnatin, nasarar da aka samu a kashi na farko ta bude hanya ga sabon shirin bashin N729bn, wanda ake sa ran zai kara samar da kudaden da ake bukata domin bunkasa dukkan bangarorin samar da wutar lantarki a Najeriya.
Verheijen ta ce gwamnati na son tabbatar da cewa ana gudanar da sauye-sauyen bangaren lantarki ne bisa gaskiya da cika alkawura, domin dawo da amincewar masu zuba jari da kuma inganta samar da wutar lantarki a kasar.
Batun gyara wutar lantrki daga minista
A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe ya yi karin haske kan yada wasu jita-jita game da gyaran wutar lantarki a kasar.
Ministan ya yana magana ne kan rahoton cewa ya yi alkawarin gyara matsalar lantarkin Najeriya cikin watanni uku yayin tantance shi.
Kakakinsa Adeola Adelabu ya ce Tegbe ya ce za a fara gyaran farko cikin kwanaki 100, amma manyan sauye-sauye za su dauki shekara guda.
Asali: Legit.ng


