Najeriya da Jamus Za Su Yi Taro na Musamman, Za Su Tattauna kan Abubuwa 3
- Najeriya da Jamus za su gudanar da muhimmin taron hadin gwiwa a Abuja domin karfafa dangantaka kan kasuwanci, tsaro da makamashi mai sabuntawa
- Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, za ta karbi takwaranta na Jamus domin tattauna sababbin hanyoyin hadin gwiwa
- Taron zai mayar da hankali kan zuba jari, fasaha, ilimi, noma, sauyin yanayi da bunkasa tattalin arziki domin amfanin kasashen guda biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Najeriya da Jamus za su gudanar da wata muhimmiyar ganawa a Abuja ranar Laraba, domin tattauna yadda za a kara fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban.
Taron zai mayar da hankali kan kasuwanci, zuba jari, makamashi mai sabuntawa, yaki da sauyin yanayi, tsaro, ilimi da fasaha.

Source: Twitter
Najeriya da Jamus za su tattauna
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar ranar Talata, Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, za ta karbi takwaranta na Jamus, Johann David Wadephul, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja, in ji rahoton Punch.
Sanarwar ta bayyana cewa ziyarar na nuna irin kyakkyawar alakar da kasashen biyu suka dade suna da ita.
Ma’aikatar ta ce dangantakar Najeriya da Jamus ta shafe shekaru da dama, kuma ta ginu ne kan mutunta juna, dimokuradiyya, hadin gwiwar tattalin arziki da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Har ila yau, ta bayyana Jamus a matsayin daya daga cikin manyan abokan hulɗar Najeriya a nahiyar Turai.
Hadin gwiwar kasashen biyu ya shafi kasuwanci, zuba jari, makamashi mai sabuntawa, noma, lafiya, ilimi, sauyin yanayi, ƙaura, fasahar zamani da harkokin tsaro.
Abubuwan da za su tattauna
Sanarwar ta ce ministocin za su duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kansu, tare da tattauna sababbin hanyoyin kara karfafa alaka.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan kara jawo masu zuba jari daga Jamus zuwa manyan bangarorin tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya
Haka kuma za su tattauna batutuwan makamashi mai tsafta, masana’antun kore, ilimin sana’o’i, horas da matasa, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire.

Source: Twitter
Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada kudirinta
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana matukar daraja dangantakarta da Jamus, tare da tabbatar da kudirinta na kara bunkasa hadin gwiwa a dukkan bangarorin da za su amfani al’ummomin kasashen biyu.
Ta ce tana sa ran tattaunawar za ta kara bude sababbin hanyoyin hadin gwiwa domin bunkasa tattalin arziki, tabbatar da zaman lafiya da kuma samar da ci gaba mai dorewa ga kasashen biyu.
Kasashen Africa da Za Su Iya Shiga Jamus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jamus ta amince wa wasu kasashe biyu daga nahiyar Afirka su shiga ƙasar ba tare da neman biza ba domin gajeren zama.
Kasar Najeriya na cikin ƙasashen Afirka da har yanzu ake bukatar ’yan ƙasarsu su nemi bizar shiga Jamus kafin su yi tafiya zuwa ƙasar.
Masu fasfon Mauritius da Seychelles za su iya shiga Jamus ba tare da biza ba, amma dole su bi sharuddan zama da dokokin ƙasar.
Asali: Legit.ng
