Ana Shirin Zaɓen 2027, Gwamna Ya Nemi Afuwar Ƴan Ƙabilar Igbo kan Yaƙin Basasa

Ana Shirin Zaɓen 2027, Gwamna Ya Nemi Afuwar Ƴan Ƙabilar Igbo kan Yaƙin Basasa

  • Ana shirin zaben shekarar 2027, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya nemi afuwar al'ummar Igbo baki daya
  • Mutfwang ya yabawa Igbo saboda gudunmawar tattalin arziki, ya bukace su su ci gaba da hada kai, su zuba jari tare da horas da matasan Plateau
  • Shugabannin al'ummar Igbo sun amince da Mutfwang a matsayin dan takararsu na gwamna a shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya nemi afuwar al'ummar Igbo kan yakin basasa da aka yi.

Mutfwang ya fadi haka ne bayan rawar da jihar ta taka a yakin basasar Najeriya, yana mai cewa an yaudari mutanen Plateau suka shiga yakin.

Gwamna Calen ya nemi afuwar kabilar Igbo
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau a gidan gwamnati. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani jawabinsa a taron tattaunawa da shugabannin al'ummar Igbo daga kananan hukumomi 17 na Plateau, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Mun daina bautawa siyasa', Fahad Dankabo ya kawo sabon salo a siyasar Kano

Gwamna ya tabo batun yakin basasa

Mutfwang ya bukaci a birne abubuwan da suka faru a baya inda ya ce tuna su zai sake dawo da abubuwa baya.

Gwamnan ya yabawa al'ummar Igbo kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Plateau, yana mai cewa suna daga cikin ginshikan ci gaban jihar.

Ya ce tun bayan kare yakin basasa, Plateau, ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi karbar al'ummar Igbo hannu bibbiyu, yana mai tunatar da cewa an biya wasu diyya saboda asarar da suka yi.

Mutfwang ya ce:

"Ina neman afuwar al'ummar Igbo domin mu bar abin da ya faru a baya, mu ci gaba da karfafa hadin kai. Mun zama daya, an yauudari mutanenmu suka shiga yaki, kuma muna nadamar hakan. Dole mu rufe wannan shafi mu ci gaba.
"Dole mu hada kai. Muna son al'ummar Igbo su dauke mu a matsayin 'yan'uwa, tare mu samar da yanayin da kowa zai samu damar cigaba."

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Gwamnan ya kuma roki 'yan kasuwar Igbo da ke Plateau su tallafa wa 'yan asalin jihar ta hanyar samar da ayyukan yi, horaswa da zuba jari domin matasa.

"Najeriya kasa ce mai girma, kuma babu wata kabila da ta nuna hazakar kasuwanci fiye da Igbo. Ina rokon ku ku yada wannan ruhin a Plateau, sannan ku dauki matasan Plateau aiki ku kuma horas da su."

- Caleb Mutfwang

Gwamna Caleb ya fadi gudunmawar Igbo a Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Facebook

Martanin shugabannin ƙabilar Igbo

A yayin taron, shugabannin al'ummar Igbo sun bayyana goyon bayansu ga Mutfwang domin ya sake tsayawa takarar gwamna a zaben 2027 saboda shugabancinsa mai hada kan jama'a da gudanar da mulki cikin adalci, cewar Vanguard.

Shugaban al'ummar Igbo a Plateau, Cif Chidi Onah, ya sanar da amincewar, yana cewa gwamnan ya nuna kwarewa, gaskiya da jajircewa wajen tabbatar da daidaito da ci gaba.

Ya ce:

"Mun amince da Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin dan takarar da al'ummar Igbo za su mara wa baya a zaben gwamna na 2027. "Mun yi hakan ne saboda kwarewarsa, mutuncinsa da shugabanci nagari."

Onah ya kara da cewa gwamnan ya inganta zaman lafiya, ya samar da yanayin da kasuwanci ke bunkasa, sannan ya tsaya tare da al'ummar Igbo lokacin rasuwar sarkinsu.

Kara karanta wannan

Matasa 9 sun rasu a hanyar neman arziki daga Sokoto zuwa Legas

Yan bindiga: Gwamna Caleb ya magantu kan sulhu

An ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya yi magana kan tattaunawa da ƴan bindiga yayin da ake fama da hare-haren ta'addanci.

Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kama wasu da ake zargi da hare-hare, yayin da bincike ke tona asirin hanyoyin sadarwar masu laifi.

Mutfwang ya ce gwamnatinsa na kudi jari a noma, ruwa da tattalin arziki domin jawo masu zuba jari da bunƙasa Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.