"Da ban Kai Labari ba"; Gwamna Mutfwang Ya Fadi Abubuwan da Suka Sa Ya Samu Nasara a Plateau

"Da ban Kai Labari ba"; Gwamna Mutfwang Ya Fadi Abubuwan da Suka Sa Ya Samu Nasara a Plateau

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana gudunmawar da ya samu kafin zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP
  • Caleb Mutfwang ya bayyana cewa wani mutum da bai sani ba, ya cika aljihunsa da kudade dab da gudanar da zaben fitar da gwani
  • Hakazalika, gwamnan ya tuna baya kan yadda hukuncin Kotun Koli ya taimake shi ya ci gaba da rike kujerar mulkin Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya tuna baya kan wasu abubuwan da suka faru a gwamnatinsa.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya dawo masa da nasararsa, shi ya ceci gwamnatinsa daga mutuwa farat ɗaya.

Gwamna Mutfwang ya ce ya samu kyautar kudi
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a lokacin taron godiya na cikar shekaru uku da kafuwar gwamnatinsa a babban cocin Church of Christ in Nations (COCIN) da ke Jos.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ajiye girma yana rokon talaka afuwa da sake zaben APC a 2027

Gwamna Caleb Mutfwang ya tuna baya

Ya bayyana cewa wani bawan Allah da bai sani ba ya ba shi kyautar dalar Amurka 100,000 kwanaki uku gabannin zaɓen fitar da gwani na kujerar gwamna na jam'iyyar PDP, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

A yau wannan kudi ya zarce N130m a kasuwar canji, sai dai a wancan lokaci dala ba ta kai haka daraja ba.

Mutfwang ya kasance a jam'iyyar PDP kafin daga baya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Gwamnan, wanda ya bayyana duka waɗannan abubuwa guda biyu a matsayin ayyukan shiga tsakani na Ubangiji, ya ce da ya rasa nasararsa da ba don hukuncin Kotun Kolin ba wanda ya mayar da shi a matsayin gwamna biyo bayan ƙalubalantar zabensa da aka yi.

"Na tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai kokarin kama shi. Da ba don Kotun Ƙoli ba, da ban kai labari ba."

- Gwamna Caleb Mutfwang

Kara karanta wannan

Taraba: Bayan na tsagin Wike, tsohon minista ya samu tikitin neman gwamnan PDP

Ya tuno da murna da farin cikin da suka biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 12 ga watan Janairu, 2024, inda ya lura cewa mata 'yan kasuwa sun yi murnar hukuncin ta hanyar ba da kayayyaki kyauta ba tare da amsar kuɗi ba.

A cewarsa, wannan lamari ya kasance ɗaya daga cikin mafi ratsa zuciya a cikin tafiyarsa ta siyasa.

Gwamna Mutfwang ya samu kyauta

Gwamnan ya kuma bayyana cewa burinsa na zama gwamna ya samu babban tallafi dab da zaɓen fitar da gwani na PDP, lokacin da wani mutum da bai taɓa haɗuwa da shi ba a rayuwarsa ya miƙa masa kyautar $100,000.

“Kwanaki uku kafin zaɓen fitar da gwani, wani da ban taɓa sani ba a rayuwata ya ba ni kyauta sannan ya ce, ‘Kada ka buɗe shi sai ka je gida.’ Lokacin da na buɗe, dalar Amurka ce $100,000."

- Caleb Mutfwang

Gwamna Mutfwang ya tuna baya
Gwamna Mutfwang na jawabi a wajen taron nuna godiya da cika shekara 3 a mulki Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Mutfwang ya ƙara bayyana cewa wani fitaccen dattijo da ke jihar Plateau ne ya ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓensa na gwamna, koda yake ya ƙi bayyana sunan mutumin ko kuma adadin kuɗin da aka kashe.

“Ɗaya daga cikin iyayen ƙasar nan ya ce da ni, ‘Ɗana.’ Ba zan faɗa muku adadin kuɗin da ya ba ni ba; wata rana zan faɗa. Shi ya biya dukkan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓena."

Kara karanta wannan

'Ba mu da zabi': Nyesom Wike ya yi magana kan sake zaben Tinubu a 2027

- Gwamna Caleb Mutfwang

Hare-haren Plateau sun damu Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya nuna damuwa game da harin da aka kai a Plateau wanda ya jawo rasa rayuka.

Gwamna Mutfwang ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen aiki tare da kama waɗanda ke da hannu a mummunan harin da aka kai al’ummar Ratatis a Dorowa Babuje, Barkin Ladi.

Mutfwang ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai kiran lamarin da ta’addanci mara dalili da kuma koma baya ga zaman lafiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng