Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF

Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF

- Kungiyar dattawan arewa sun yi wani gagarumin zargi a kan mutanen kudu maso gabas

- Shugaban kungiyar, Ango Abdullahi ya bayyana cewa yan kabilar Igbo na farma yan arewa a kudu

- Shugaban na NEF ya ce kungiyar za ta ziyarci kudu maso gabas don tattaunawa da gwamnoni a yankin kan damuwarsu

Kungiyar dattawan arewa ta yi zargin cewa yan Igbo ne ke aiwatar da mafi akasarin hare-hare da ake kai wa yan arewa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shugaban kungiyar ta NEF, Farfesa Ango Abdullahi, ne yayi zargin a yau Talata, 8 ga watan Disamba, a Port Harcourt, jihar Ribas.

A cewar rahoton, shugabannin na NEF na wani rangadi ga al’umman arewa a fadin kasar biyo byan zanga-zangar EndSARS.

Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF
Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na cikin ganawa da dukka gwamnonin Nigeria 36

Abdullahi ya ce:

“Ya fara bayyana karara cewa mafi akasarin farmakin da ake kaiwa yan arewa a yankuna daban daban na kudu yana fitowa ne daga wajen mutanen jihohin kudu maso gabas.”

A wani lamari makamancin haka, Kungiyar matasan tare ta NYLF na kasa, tayi gargadin cewa ta sanar da mambobinta a fadin jihohin arewacin Najeriya da Abuja, kan su shirya yin gaba-da-gaba da duk wasu mutane da suka shirya zanga zangar EndSARS na biyu.

Kungiyar ta ce zanga zangar ta kere fa’idarta, cewa ba za ta zuba ido ta kyale wasu su jefa yan Najeriya cikin wani kangin rayuwa ba a yayinda ake tsaka da matsin tattalin arziki.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamrad Elliot Afiyo ya ce bata gari sun kwace rukunin farko na zanga zangar wanda ya jefa kasar cikin koma bayan tattalin arziki, inda ya kara da cewa NYLF ba za ta bari a maimaita wani zanga zanga ba a jihohin arewa 19.

A wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bude iyakokin Najeriya.

Ya bayyana hakan ga gwamnonin Najeriya 36 a ganawar da yayi da su ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

Buhari ya ce ya rufe iyakokin ne domin hana fasa kwabrin makamai da kwayoyi amma tun da yanzu makwabtan Najeriya sun hankalta, zai iya bude wa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel