Gwamnatin Tinubu Tayi Maganar Yadda Za a Raba Rijiyoyin Mai a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Tayi Maganar Yadda Za a Raba Rijiyoyin Mai a Najeriya

  • Hukumar NUPRC za ta bada lasisin hako rijiyoyin mai, sai dai wannan karo ba kudin da aka sa za a duba ba
  • Kamfanoni 286 ne suka shiga takarar a matakin farko a Legas, amma yanzu 196 ne suka kai mataki na gaba
  • Daga cikin kamfanonin da suka tsallake, guda 143 sun mika takardun tayi sama da 200 na neman lasisi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi karin haske game da yadda za a yi rabon rijiyoyi ko tubalen mai da ake shirin yi kwanan nan a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ‘yan kasuwa cewa ba daga mutum ya sa kudin da ya fi na kowa yawa shikenan zai samu rijiya ba.

Rijiyoyin Mai
Wata matatar mai da kuma ma'aikata a rijiyoyin mai a Bayelsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sabon tsari wajen rabon rijiyoyin mai

Jaridar Punch ta ce gwamnati za ta yi la’akari da cancantar aiki da kuma kwarewa wurin hakan man kafin a damka wa wani rijiya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Shugabar hukumar NUPRC na kasa, Oritsemeyiwa Eyesan ta yi bayani cewa an kawo wannan tsari ne da nufin yin abin da ya dace.

Oritsemeyiwa Eyesan ta ce gwamnati ba ta so a ba mutum rijiyar mai amma ya bar ta haka nan ba tare da an harko mai ko gas ba.

Idan an tashi rabo irin haka, a kan samu wasu ‘yan kasuwa da za su narka kudin da ya fi na kowa saboda kawai a sallama masu rijiyoyi.

NUPRC ta tabbatar da za su bi a hankali kuma su yi aiki da gaskiya domin ganin hukumar ta yi abin da ya dace da masana’antar man.

Ban da kudin da suka sa, gwamnatin Najeriya ta yi duba ga kwarewa da sanin aikin kamfanonin da lokacin da za su dauka ana aikin hakon.

Rijiyar mai
Wani yanki da ake aikin tace danyen mai a jihar Rivers Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A 2025 aka bude damar samun lasisin rijiyar mai

A Nuwamban 2025 aka bude damar bada lasisin rijiyoyin mai da gas har 50. Wannan lamari ya yi daidai da dokar harkokin mai na 2021.

Shafin ya kasance a bude har zuwa lokacin da aka kammala rajista a watan Fubrairun 2027.

Kara karanta wannan

Bam din Iran ya tashi da sojan Amurka, ya mutu har lahira

Cikin rijiyoyi 50 da ke kasuwa, akwai 34 da suke yankin Neja-Delta. Daga cikinsu akwai 16 da ke kasan ruwa sai 18 da ke bakin gaba.

Tashar CNBC Africa ta rahoto cewa sauran rijiyoyin 16 suna a wasu yankuna ne na dabam.

A cikin kamfanoni 286 da suka shiga neman rijiyoyin man tun farko, NUPRC ta amince da 196 wadanda za su kara da junansu a yanzu.

Man fetur zai kara tsada a Najeriya

An samu rahoto 'yan kasuwa masu shigo da fetur a Najeriya sun yi haramar ƙara farashin litar mai daga ₦1,230 zuwa ₦1,350 a tashoshi.

Wannan ƙarin farashin ya faru ne sakamakon tsadar mai da matsalar sufurin ruwa a kasuwar duniya wanda rikicin Amurka da Iran ya haifar.

Sabon farashin zai shafi gidajen mai na ƙasar duk da cewa hukumar NMDPRA ta ba kamfanoni masu zaman kansu lasisin shigo da kaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng