"Gwamnati Za Ta Sayar da Rijiyoyin Mai Ga ’Yan Kasuwa Kadai", Inji Ministan Tinubu

"Gwamnati Za Ta Sayar da Rijiyoyin Mai Ga ’Yan Kasuwa Kadai", Inji Ministan Tinubu

  • Gwamnatin tarayya za ta sayar da rijiyoyin man fetur 17 ga manyan 'yan kasuwa da ke da karfin jari da fasahar tafiyar da rijiyoyin
  • Karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce wannan karon ba za a sayar da rijiyoyin ga 'yan siyasa ba
  • Sanata Lokpobiri ya koka kan yadda da yawa daga cikin rijiyoyin da aka mallaka wa mutane a shekaru uku baya, sun daina bayar da riba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce gwamnatin tarayya za ta sayar da rijiyoyin mai 17 a yayin sabunta lasisin rijiyoyin na 2024.

Sai dai Sanata Lokpobiri ya jaddada cewa 'yan kasuwa da ke da karfin jari da fasahar tafiyar da rijiyoyin ne za a sayarwa ba wai 'yan siyasa ba.

Kara karanta wannan

"Ban san da zamanku ba", Fubara ya yi kakkausar suka ga 'yan majalisar Rivers

Gwamnati za ta sayar da rijiyoyin mai 17
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin sayar da rijiyoyin mai 17 ga 'yan kasuwa. Hoto: @senlokpobiri
Asali: UGC

Channels TV ta ruwaito karamin ministan ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar fasahar man fetur ta Najeriya (PETAN) ta shirya a Texas, kasar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Lokpobiri ya gana da kungiyar PETAN ne a yayin da ake ci gaba da taron fasahar duniya na 2024 da ke gudana a yanzu haka.

Gwamnati ba ta amfana da rijiyoyin mai

A cewarsa, matakin sayar da rijiyoyin man ga 'yan kasuwa ya kasance wani bangare na yunkurin zuba jari da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ministan ya bayyana cewa, a baya, ana sayar da rijiyoyin man ne ga wadanda suke nema, wanda hakan ya jawo koma baya na akalla kashi 90 na kula da rijiyoyin man.

Wannan, in ji shi, ya hana gwamnati cin gajiyar ainihin abin da rijiyoyin ya kamata su samar domin an sayar da su ne ba tare da la'akari da fasaha ko karfin kudin tafiyar da su ba.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda likitan boge ke zubar da ciki ga ‘yan mata a Filato kan N5,000

"Rijiyoyin mai na 'yan kasuwa ne" - Lokpobiri

Game da kokarin gwamnatin tarayya na canja tsarin sayar da rijiyoyin mai, jaridar The Punch ta ruwaito karamin ministan man fetur din yana cewa:

"“Mun lura da tarin rijiyoyin mai marasa aiki kuma ba wani jari da aka zuba musu a cikin shekaru ukun da suka gabata.
"A game da wannan, ba za mu ƙara lamuntar hakan ba, domin haka, waɗanda ke neman mallakar rijiyoyin mai dole ne su kasance masu karfin kuɗi da fasahar iya tafiyar da rijiyoyin.
"Wadannan rijiyoyin ba na 'yan siyasa ba ne. Muna neman 'yan kasuwa ne da ke da karfin jari da kuma fasahar gudanar da ayyukan rijiyoyin yadda ya kamata."

Gwamnati za ta kwace lasisin rijiyoyin mai

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito karamin ministan albarkatun man fetur na kasa, Sanata Heineken Lokpobiri ya ce gwamnati za ta kwace lasisin masu rijiyoyin mai.

Sanata Heineken Lokpobiri ya ce za a kwace lasisin gudanarwar da aka ba masu rijiyoyin man da ba basa kai wa gwamnati haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel