Gwamnatin Tarayya ta yi Barazanar Kwace Lasisin Rijiyoyin Mai kan Rashin Biyan Haraji

Gwamnatin Tarayya ta yi Barazanar Kwace Lasisin Rijiyoyin Mai kan Rashin Biyan Haraji

  • Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin da ta bawa wasu daidaikun jama'a da kamfanonin da ba sa kawowa kasar nan haraji
  • karamin Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan inda a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Legas
  • Rijiyoyin da za a iya kwace lasisin gudanarwar da gwamnati ta basu su ne wadanda kawo basa kawowa haraji ga gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Legas- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar da kwace lasisin rijiyoyin mai da ba a amfani da su daga hannun kamfanoni da daidaikun mutane saboda rashin samun kudin shiga.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur ta jawo tashin farashin motoci da sauran abubuwan hawa

Karamin ministan ma’adanan man fetur, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a jihar Legas a wani taro da Petroleum Club ta shirya.

Asiwaju Bola Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta yi Barazanar Kwace wasu Lasisin Rijiyoyin Man fetur Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

A cewar Heineken Lokpobiri, kasar nan ta yi asarar dala biliyan 30 a cikin shekaru biyu da rabin da suka gabata, kamar yadda Punch Newspapers ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin na damuwa da asarar fetur

Ministan ya kara da bayyana damuwar yadda masu rike da lasisin kuma ba sa hako man fetur din da cewa suna janyowa Najeriya asara, kamar yadda punch din ta ruwaito.

Heineken Lokpobiri ya kara da cewa dambarwar Seplat/ExxonMobil yana janyowa gwamnatin tarayya asarar gangar mai 480,000.

Sai dai ya bayyana fatan idan gyara dukkanin matatun man fetur din kasar nan domin bunkasa tace man a cikin gida.

Kara karanta wannan

Yadda rashin ruwa yake barazana ga rayuwa da masu sana'o'i a jihar Sokoto

“Ina sa ran gyara matatun manmu dake Port Harcourt a Warri, da na Kaduna. Yanzu da matatar man Dangote ke tasowa, da kuma wasu kananan matatun mai da muka bawa lasisi (a shirye na kara bayar da wasu), za mu iya tace man da muka sha ba wai a Najeriya kawai ba har baki dayan yankin Afrika ta yamma," Heineken Lokpobiri

Ana gyaran matatar man Kaduna, Minista

A shekarar 2023 ne gwamnatin tarayya ta ce ana aiki gadan-gadan domin kammala gyaran matatar man dake jihar Kaduna domin fara tace gurbataccen mai a cikin kasar nan.

Karamin ministan albarkatun mai a kasar, Heineken Lokpobiri ya ba da tabbacin bayan kai ziyarar gani da ido kan aikin matatar a karshen shekarar 2024.

Ya ce matatar man ta zamani za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar man fetur a kasar nan idan ta kammala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel