Bam Din Iran Ya Tashi da Sojan Amurka, Ya Mutu har Lahira
- Rahoto ya nuna cewa rundunar sojin Amurka ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin dakarunta a arewacin Iraq
- Mutuwar sojan ta kara yawan adadin sojojin Amurka da suka rasa rayukansu a yakin da ake da Iran zuwa mutum 17
- Firaministan Iraq na shirin ziyartar birnin Tehran bayan ganawarsa da shugaban Amurka Donald Trump a Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rundunar Amurka ta CENTCOM ta bayyana cewa sojan ta ya rasu a ranar 18 ga watan Yuli a lokacin da yake lalata bama-baman da ke jikin jirgin yakin Iran.
CENTCOM ta kara da cewa wani sojan daban ya raunana, amma yana ci gaba da karbar magani saboda raunin da yake da shi ba mai tsanani ba ne.

Source: Facebook
An gano sassan jikin mutum
CNN ta rahoto cewa rundunar ta kuma bayyana cewa ta gano sassan jikin dan adam a kasar Jordan bayan da a baya aka lissafa wani soja a matsayin wanda ya bace yayin fafatawa.
Zuwa yanzu ba a tabbatar ko sassan jikin na sojan Amurka da ya ba ce ba ne, amma an ce bincike zai tabbatar da gaskiyar lamarin daga baya.
A yanzu haka dai sojojin Amurka uke ne suka riga mu gidan gaskiya tun bayan sabon yakin da ya barke tsakanin Iran da Amurka.
Hakan ya kara yawan adadin dakarun kasar Amurka da suka rasa rayukansu zuwa mutum 17 a cikin wannan yaki da ke daf da cika watanni biyar ana fafatawa.
Ziyarar Firaministan Iraq Tehran
Rahoton Middle East Eye ya nuna cewa Firaministan kasar Iraq, Ali Al-Zaidi, yana shirin tafiya birnin Tehran a mako mai zuwa domin gudanar da tattaunawa ta sirri da shugabannin Iran.
Wannan ziyara tana zuwa ne kwanaki kadan bayan Al-Zaidi ya gana da Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, a fadar White House da ke Washington.

Source: Getty Images
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iraq ta bayyana a ranar Lahadi cewa ziyarar za ta maida hankali ne kan kulla yarjejeniyoyi daban-daban don inganta dangantaka da kare muradun juna.
Ziyarar tana zuwa ne a lokaci mai muhimmanci da kasar Iraq ke kokarin daidaita dangantakarta tsakanin Amurka da kuma makwabciyarta Iran.
Batun rage dogaro da Amurka
A makon da ya gabata, Firaministan kasar ta Iraq ya sanar cewa sojojin Amurka za su fice daga kasar kafin ranar 30 ga watan Satumban 2026.
Ya kara da cewa kungiyoyin mayakan da Iran ke goyon baya ba za su sami wani dalilin ci gaba da rike makamai ko gudanar da ayyukansu ba bayan ficewar Amurkan.
Kasar Iraq ta dade tana taka rawar tsani tsakanin Amurka da Iran domin kwantar da tarzoma da hana tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta gargadi 'yan kasarta
A wani labarin, mun kawo muku cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya kasashe 23 a cikin jerin matakin tsaro mafi haɗari mai suna 'Level 4.
A sabon gargadin da ma'aikatar ta fitar a makon daya wuce, ta gargadi 'yan Amurka da kada su sake kai ziyara wadannan kasashen saboda matsalar tsaro.
Kasashen da aka lissafa sun hada da Iran, Rasha da kuma wasu ƙasashe 11 a nahiyar Afirka da suka hada da Jamhuriyar Nijar da sauransu.
Asali: Legit.ng

