An Fitar Mukamai 26 da Tinubu Ya ba Mutane Daban Daban a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa mutane 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10 domin inganta ayyukan gwamnati
- Tsohon gwamna Ayo Fayose, ya zama shugaban Hukumar REA, yayin da Manjo Janar Junaid Bindawa ya jagoranci Hukumar Albashi
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa dukkan sababbin naɗe-naɗen za su fara aiki nan take bayan amincewar shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗa mutane 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10, a wani mataki na cike guraben shugabanci da ƙarfafa ayyukan hukumomin gwamnati.
Sanarwar ta fito ne daga mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar 20 ga Yulin 2026.

Source: Facebook
Onanuga ya wallafa a Facebook cewa Daga cikin naɗe-naɗen, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya zama shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara (REA).
Waɗanda Bola Tinubu ya naɗa
Shugaba Tinubu ya kuma naɗa Alhaji Ahmadu Abubakar da Ilyasu Ibrahim Makinta a matsayin mambobi kuma daraktoci marasa zartarwa a hukumar REA.
Babban Daraktan hukumar, Abba Abubakar Aliyu, da daraktocin zartarwa uku da aka naɗa tun da farko za su ci gaba da zama cikin kwamitin gudanarwa.
A Hukumar Albashi da Tsarin Albashi ta Ƙasa kuwa, Olajumoke Okoya-Thomas, tsohuwar 'yar majalisar wakilai daga Legas, ta zama sakatariyar hukumar.
Haka kuma, Dr. Ogbole Ene Lilian da Oladele Olatubosun da Yakubu Umar Barde sun zama kwamishinoni masu wakiltar jihohin Benue da Oyo da Kaduna.
Sauran muƙaman da aka nada
Shugaban ƙasar ya kuma sauya Tosin Johnson Adeyanju daga Asusun Tallafawa Caca na Ƙasa (NLTF) zuwa Hukumar Tara Kuɗin Shiga da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi a matsayin sakatare.

Kara karanta wannan
Gombe: Tafiyar Pantami ta kara karfi, mutanen Sanata Bayero Nafada sun tsaya a PDP
Haka kuma, an naɗa Dr. Abuh Mohammed a matsayin Babban Darakta na Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NPC), yayin da Dr. Akinola Odeyemi ya zama Darakta na Kamfanin NBET.
An kuma naɗa Dr. Anthony Inalegwu Godwin a matsayin shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya, yayin da Injiniya Julius Oloro ya zama shugaban Cibiyar Kera Kayan Aikin Noma ta Ƙasa da ke Ilorin.
Punch ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya kafa sabon kwamitin Hukumar Kula da Alhakin Kasafin Kuɗi ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Maikano Saidu.

Source: Facebook
Sannan Shuni Muhammad Dahiru ya zama sabon Sakataren Zartarwa na Hukumar Ilimin Manya da Ilimin Bai-ɗaya, yayin da Gisaor Vincent Iorja ya maye gurbin Mathias Byuan a Hukumar Gidaje ta Tarayya.
'Za a kifar da Tinubu,' ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwar cewa haɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, za kifar da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce 'yan Najeriya da suka sha wahala a ƙarƙashin gwamnatin APC za su sauya gwamnati.
Bolaji Abdullahi ya yi magana yana mai cewa ADC ce kaɗai ke wakiltar sahihin madadin gwamnati a halin yanzu kuma za a zabe ya a 2027.
Asali: Legit.ng
