Kanin Tsohon Gwamna da Tinubu Ya Ba Mukami Ya Ba Shi Shawarar Watsi da Kujerar

Kanin Tsohon Gwamna da Tinubu Ya Ba Mukami Ya Ba Shi Shawarar Watsi da Kujerar

  • Shugaba Tinubu ya nada tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya shugabanci majalisar da ke kula da hukumar REA
  • Isaac Fayose ya zargi gwamnati da yin nadin saboda tsoron alakar da ke tsakaninsu da Peter Obi ganin ya ziyarce shi
  • Kanin tsohon gwamnan ya tunatar da mutane yayansa ya taba alkarawarin ba zai sake karbar irin wannan mukamin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ekiti - Isaac Fayose wanda kani ne a wajen Ayo Fayose ya yi kira ga yayansa da ya yi watsi da kujerar da aka ba shi a REA.

Duk da yana karkashin jam’iyyar adawa, Bola Ahmed Tinubu ya zabo Ayo Fayose da ya tashi rabon wasu mukamai a gwamnati.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Ayo Fayose a shekarun baya a Ekiti Hoto: Getty Images/Inside Port Harcourt
Source: UGC

Isaac Fayose ya soki nadin mukamin da aka yi

An ji Isaac Fayose a shafinsa na Instagram yana ganin yayansa ya fi karfin zama shugaban majalisar da ke kula da harkokin REA.

Kara karanta wannan

'Ko makiyana sun san ni ke da Kano,' Kwankwaso ya yi martani ga Ali Modu Sheriff

A ranar Litinin 20 ga Yuli 2026 Fayose ya fito yana sharhi game da mukamin da aka ba tsohon gwamnan da wasu mutane 26.

Matashin ya jefa tambaya cewa meyasa ba a ba tsohon gwamnan na jihar Ekiti babban mukami ba sai kujera a hukumar REA.

Isaac Fayose ya ce:

“Sun ce an ba yaya na kujerar Darekta Janar, ba minista, ba ambasada ba,”
“Sun ce an ba shi Darekta Janar, shugaban hukuma, shugaban kwamiti. Ba su ga minista da za su ba shi, ba su ba shi jakada ba"

Tinubu: Isaac Fayose ya raina kujerar REA

A bayaninsa, Leadership ta rahoto yana cewa har Reno Omokri ya samu kujerar jakada zuwa kasar waje a gwamnatin Bola Tinubu.

“Ko Reno Omokri dai, sun ba shi kujerar jakada. Ba su iya ba ‘danuwana mukamin jakada ba. Meyasa sai wani shugaban hukuma?”

Bayan nan Isaac ya bukaci sanin mene ne dalilin fitar da mukamin ‘yan kwanaki bayan shi ya zauna da ‘dan takaran NDC, Peter Obi.

Lokacin da Obi mai neman zama shugaban kasa ya ziyarci Isaac Fayose, an ji shi yana kiran ‘dan siyasar da shugaban kasa mai jiran gado’

Kara karanta wannan

Ministan PDP ya fadi abin da ya sa Peter Obi ya doke Tinubu a Legas a zaben 2023

“Meyasa ba su ba ka mukamin tun tuni ba? Meyasa suka jira sai da Obi ya zo?”

Sannan an ji shi yana cewa da Ayodele Peter Fayose zai bar ofis, ya fada masa cewa ba zai karbi kujerar minista, DG ko ya zama sanata ba.

Kafin barin mulki ya ce kasuwancinsa zai sa a gabansa don haka Isaac ya ba shi shawarar ya rabu da kujerar nan, ya mika wa ‘dan da ya haifa.

“Ina taya ka murnar nadin mukaminka. Gara ka ba ‘dan ka. Ka da ka hau irin wannan kujera. Ka fi karfin wannan…”

Abin da ya ci Tinubu a Legas a 2023

An ji abin da ya sa a 2023 LP ta doke Bola Tinubu a Legas a rahoton wata hira da aka yi da tsohon ministan tsaro, Ambasada Musiliu Obanikoro.

'Dan siyasar yana ganin tikitin Musulmi da Muslim da APC ta yi a zaben da ya gabata shi ne ya jawo kiristoci suka ki zaben Tinubu a jihar Legas.

Musiliu Obanikoro ya ce daga cikin abin da ke nuna saukin ra’ayin Bola Tinubu a addini shi ne yadda ‘dansa Seyi ya bar Musulunci ya zama kirista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng