Borno: Bayan Rahoton Kai Hari Makarantar Mata, Gwamnati Ta Fayyace Gaskiya

Borno: Bayan Rahoton Kai Hari Makarantar Mata, Gwamnati Ta Fayyace Gaskiya

  • Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi tir da yadda rahotanni suka rika cewa an kai hari Kwalejin 'Yan Mata ta Tarayya (FGGC) da ke Monguno a jihar Borno
  • Ta bayyana cewa duk da akwai maganar an kai hari, amma lamarin bai shafi daliban da ke makarnatar tarayya ta 'yan matan da ake cewa ba
  • Gwamnati ta tabbatar da cewa dukkan ɗalibai, malamai da kayan makarantar suna cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya ɓace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an kai hari Kwalejin 'Yan Mata ta Tarayya (FGGC) da ke Monguno a jihar Borno.

Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a ta ma'aikatar, Folasade Boriowo, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Litinin 20 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Gwamnati ta yi magana kan kai hari makarantar yan mata a Borno
Shugaban kasa Bola Tinubu, Gwamnan Borno Babagana Zulum Hoto: Bayo Onanuga/The Governor of Borno state
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa a cikin sanarwar, ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya zai iya haddasa fargaba mara amfani ga iyaye, masu kula da yara da sauran jama'a.

Gwamnati ta karyata an kai hari Borno

A ruwayar The Nation, babu wani hari da aka kai makarantar, kuma dukkan ɗalibai, malamai da ma'aikata suna cikin ƙoshin lafiya. Haka kuma, wuraren kwanan ɗalibai da sauran kayayyakin makarantar suna nan kalau.

Ministan ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da karatu da sauran ayyukan makaranta ba tare da wata matsala ba, cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.

Alausa ya sake jaddada cewa kare rayuka da jin daɗin ɗaliban makarantun gwamnatin tarayya na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sa a gaba.

Ya bayyana cewa FGGC Monguno na karkashin ingantaccen tsarin tsaro domin tabbatar da kariyar ɗalibai, malamai da dukiyoyin makarantar.

Kara karanta wannan

Jigo a Jam'iyyar APC ya ruga Amurka roko wa Najeriya iri

Gwamnati ta fadi wanda hari ya shafa

Ministan ya kara da cewa mutanen da lamarin ya shafa ɗaliban ajin share fage ne da ba sa cikin kwalejin, kuma gwamnatin jihar Borno ta riga ta fara ɗaukar matakan tabbatar da tsaro da walwalarsu.

Alausa ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai, masu amfani da kafafen sada zumunta, masu rubutun yanar gizo da sauran masu wallafa bayanai su tabbatar da sahihancin labarai daga amintattun majiyoyi kafin su yaɗa su.

Ma'aikatar ilimi tace gwamnatin Borno na kokari a kan daliban da aka kai wa hari
Gwamna Babagana Zuluma gidan gwamnatin jihar Borno Hoto: The Governor of Borno State
Source: Twitter

Ya ce yaɗa bayanan da ba a tantance ba na iya yaudarar jama'a, haifar da fargaba ba tare da dalili ba, rage amincewa da hukumomi tare da kawo cikas ga ƙoƙarin samar da ingantaccen yanayin karatu mai cike da tsaro.

Haka kuma ya roƙi iyaye da masu kula da yara su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar musu da cewa babu wata barazanar tsaro da ke fuskantar FGGC Monguno.

Sojoji sun kama babban 'dan ta'adda a Borno

A baya, kun samu labarin cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kama wani ɗan Sudan da wasu mutum uku da ake zargi da taimaka wa ƙungiyar ISWAP a jihohhin Arewa maso Gabas na Borno da Yobe.

Kara karanta wannan

Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu

Sojoji sun ce bayanan sirri ne suka taimaka wajen cafke waɗanda ake zargi, tare da ƙwato kayayyakin da ake zargin na tallafa wa ayyukan ta'addanci a yankunan da ke fama da matsalar tsaro da ta'addanci.

Dakarun sun ce nasarar ta nuna ci gaban da ake samu wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje da karya hanyoyin tallafa wa kungiyar yan ta'addan ISWAP da keci gaba da kokarin hana jama'a zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng