Miyetti Allah Ta Nemi a Saki Shugabanta nan Take, Ta Yi Kira ga Tinubu
- Fulani makiyaya sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin Najeriya su sa baki domin a saki shugabansu, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo
- Sun ce an taba kama Bello Bodejo sau uku tun daga shekarar 2024, inda suka ce a lokuta biyu da suka gabata an janye tuhuma a kansa
- Kungiyar Fulanin ta buƙaci a tabbatar an masa adalci, an bi doka da kare haƙƙin Bodejo kamar yadda ya kmata a yi wa kowane dan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ya fara kira da a saki shugabanta na kasa, Alhaji Bello Bodejo da aka kama.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Bello Bodejo ne kwanakin baya saboda wasu zarge-zargen kudi bayan ya nuna cewa zai fito takarar Sanata.

Source: Twitter
An nemi sakin Bello Bodejo
Shugaban kungiyar Miyetti Allah shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Nasiru Liman Jalbu ne ya yi kira a saki Bello Bodejo a wani sako da aka wallafa a shafin kungiyar na Facebook.
Sanarwar da ya fitar ta ce:
"Shugabanni da mambobin al'ummomin Fulani makiyaya a faɗin Najeriya suna roƙon mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR; mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro; lauyan Tarayya kuma ministan shari'a; shugaban jam'iyyar APC na ƙasa; da sauran hukumomin da abin ya shafa da su sa baki kan ci gaba da tsare jagoransu, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo."
Yaushe aka kama Bodejo?
Game da kama Alhaji Bello Bodejo da hukumomin Najeriya suka yi, sanarwar kungiyar Miyetti Allah ta ce:
"Mun tuna cewa an fara kama Alhaji Bello Bodejo ne a ranar 23 ga Janairu, 2024, dangane da batutuwan da suka shafi kafa wata ƙungiyar sintiri ta makiyaya wadda gwamnatin jihar Nasarawa ta ɗauki nauyin kafawa."
"Bayan watanni ana shari'a, an sake shi tare da janye dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.
"Daga baya, a ranar 9 ga Nuwamba, 2024, jami'an tsaro sun sake kama shi, sannan aka sake shi bayan an warware batun tare da sake janye tuhume-tuhumen da ake masa."
"Kwanan nan, a ranar 8 ga Mayu, 2026, an ruwaito cewa hukumar DSS ta kama shi a Jalingo, jihar Taraba, kafin daga bisani a mayar da shi hannun hukumar EFCC bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam'iyyar APC a babban zaɓen 2027."

Source: Facebook
Kungiyar Miyetti Allah ta bukaci shugabannin da ke kula da shari'ar da su tabbatar an yi wa shugabansu adalci kasancewar shi ma dan Najeriya ne.
An kashe shugaban Fulani
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mutane dauke da makamai sun kashe shugaban kungiyar Fulani makiyaya a jihar Benue.
An kashe shugaban Fulani mai sun Ardo Risku ne tare da abokin shi bayan sun halarci wani taron zaman lafiya da shugabannin yankin da ya ke.
Biyo bayan lamarin, 'yan sanda sun dukufa neman wadanda suka aikata laifin, inda bayan kwanaki aka sanar da cewa an kama mutum 10.
Asali: Legit.ng

