Majalisar Dinkin Duniya Ta Fallasa Sabuwar Dabarar 'Yan Ta'adda a Arewa
- Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kungiyoyin ta'addanci da ke aiki a Arewacin Najeriya da yankin Sahel na kara amfani da jiragen sama marasa matuki a kai hari
- Hakan nan ana zargin yan ta'addan suna amfani da fasahohin sadarwa na zamani sarrafa kudin zamani wajen gudanar da miyagun ayyukansu a sassan Arewacin kasar
- Majalisar ta ce duk da haka, akwai wasu hanyoyi da za a iya bi wajen magance matsaolin tsaro da su ka addabi yankin Arewa a Najeriya da sauran sassan Afrika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kungiyoyin ta'addanci da ke Arewacin Najeriya da sauran kasashen Yammacin Affrika da yankin Sahel na kara amfani da sabbin fasahohi wajen gudanar da ayyukansu.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Leonardo Simão, wakilin babban sakataren majalisar na musamman a Yammacin Afrika da yankin Sahel, yayin da yake gabatar da rahoto a gaban Kwamitin Tsaronsu.

Source: Getty Images
The Cable ta kawo laarin cewa rahoton ya kunshi abubuwan da suka faru tsakanin ranar 29 ga Nuwamban 2025 zuwa 30 ga Yunin 2026, inda kwamitin ya tattauna halin siyasa, tsaro da kuma matsalar jin kai a yankin.
Yan ta'adda sun canja dabara
Jaridar This day ta kawolabarin cewa Simão ya ce kungiyoyin masu dauke da makamai na kara amfani da jiragen sama marasa matuki, na'urorin sadarwa masu inganci da kuma kudaden kirifto.
Ya ce su na aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin kasa da kasa, domin mallakar yankuna da hanyoyin samun kudi tare da raunana amincewar jama'a ga hukumomin gwamnati.
Ya ce:
"Matsalar ta fi tsanani musamman a yankin tsakiyar Sahel da kuma Arewacin Najeriya."
Jami'in majalisar ya ce Najeriya, Nijar da Burkina Faso na ci gaba da fuskantar hare haren ta'addanci, garkuwa da mutane da kuma yawan mutuwar fararen hula.
Majalisar dinkin duniya: 'Jama'a sun rasa matsugunisu'
A cewarsa, kimanin mutane miliyan 6.8 sun rasa matsugunansu a yankin, yayin da wasu miliyan 1.28 suka tsallaka zuwa wasu kasashe a matsayin 'yan gudun hijira ko masu neman mafaka.

Source: Getty Images
Ya kara da cewa mata, yara da matasa ne suka fi shan wahala saboda rashin tsaro da kuma karancin kudaden tallafin jin kai.
Sai dai Simão ya yabawa wasu matakan hadin gwiwar kasashen yankin, ciki har da sake bude iyakar Kamba tsakanin Najeriya da Nijar da kuma ci gaban da aka samu wajen aiwatar da hukuncin Kotun Duniya kan rikicin iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar ECOWAS na kokarin sake farfado da rundunar ko-ta-kwana ta yankin, amma tana fuskantar matsalar karancin kudade.
'Yan Arewa su na amfana da batun tsaro
A baya, mun kawo labarin cewa rahotanni sun nuna cewa ƙasar Amurka na ci gaba da tallafawa Najeriya wajen bunkasa ababen more rayuwa da harkokin makamashi domin cicciba kasar.
Hukumar Kasuwanci da Raya Kasa ta Amurka (USTDA) na tallafawa kasashe da dama ciki har da Najeriya a fannoni daban-daban Najeriya na daga cikin kasashen da tsarin ya fara bayyana.
Daya daga cikin manyan ayyukan da USTDA ta tallafa shi ne aikin Powergas, wanda ya shafi gina karamin tashar adana iskar gas (LNG) domin karfafa iskar gas a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng

