Dubu Ta Cika: Ƴan Sanda Sun Cafke Mayakan Lakurawa da ke Addabar Garuruwan Arewa

Dubu Ta Cika: Ƴan Sanda Sun Cafke Mayakan Lakurawa da ke Addabar Garuruwan Arewa

  • Rundunar 'yan sandan Sokoto ta kama mutum bakwai da ake zargi da ta'addanci da garkuwa da mutane a samame da ta kai a sassa daban-daban na jihar
  • Wasu daga cikin wadanda aka kama sun amsa kasancewa mambobin kungiyar Lakurawa da ke addabar Silame, Binji, Tangaza, Illela da sassan Kebbi
  • Kwamishinan 'yan sandan Sokoto ya ce an gurfanar da dukkan wadanda ake zargi a kotu, yayin da bincike ke ci gaba da cafke sauran abokan aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta sanar da kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci, kungiyar Lakurawa da kuma garkuwa da mutane a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Hayatu Hassan Shaffa, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar ranar 16 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Rana ta baci: Ƴan bindiga sun yi arba da ƴan sanda bayan sun sace mutane a Sokoto

'Yan sanda sun kama wasu mayakan Lakurawa da masu garkuwa da mutane
Jami'an 'yan sandan Najeriya suna hawa tsaunuka a kokarin yaki da 'yan ta'adda. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

A yayin taron, wanda wakilin Legit Hausa ya halarta, kwamishinan ya yi karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a fannin yaki da manyan laifuka daga watan Mayu zuwa yanzu.

An kama 'yan ta'adda a Tureta

A cewarsa, samamen da jami'an rundunar suka gudanar tare da wasu hukumomin tsaro ya taimaka wajen cafke wadanda ake zargi da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

CP Shaffa ya ce a ranar 8 ga watan Yuni, 2026, jami'an 'yan sanda da ke sintiri a karamar hukumar Tureta sun kama Abu Jabbi Gero daga kauyen Kayama yayin binciken ababen hawa.

Ya ce an same shi dauke da adda, wayar salula kirar Tecno, katin SIM da kuma kudin da yawansu ya kai N60,100.

Bayan kammala bincike, rundunar ta gurfanar da wanda ake zargin a kotu domin fuskantar hukunci.

Mutum 3 sun amsa cewa su Lakurawa ne

Kwamishinan ya ce a wannan rana, jami'an 'yan sanda tare da rundunar PMF, masu yaki da garkuwa da mutane da jami'an Community Guards Corps sun kai samame maboyar masu laifi a kauyukan Matabare, Masara, Bula da Gingel a karamar hukumar Binji.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rikata 'yan Boko Haram a kananan hukumomin Borno 5

A yayin samamen, an kama Auwalu Hantsi, Faruku Gado da Ausa Magaji.

Ya ce yayin gudanar da bincike, mutanen ukun sun amsa cewa suna cikin kungiyar Lakurawa da ke addabar kananan hukumomin Silame, Binji, Tangaza, Illela da wasu yankunan jihar Kebbi.

Bayan kammala binciken da ya kamata, rundunar ta tabbatar da cewa an gurfanar da su a kotu domin fara shari'arsu.

An kama mutum 3 kan zargin garkuwa

Har ila yau, CP Shaffa ya ce a ranar 19 ga watan Yuni, 2026, rundunar ta samu bayanin sirri daga wani mai kishin kasa cewa akwai wasu mutane uku masu motsi cikin yanayi mai tayar da hankali a tashar mota ta Sokoto Central Motor Park.

Nan take jami'an Strike Force suka isa wurin tare da cafke Ummaru Abubakar, wanda aka fi sani da Mai Yaki, Shehu Garba da Aliyu Hashimu.

An kama 'yan ta'addar Lakurawa a Sokoto
Kwamishinan 'yan sandan Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa yayin magana da 'yan jarida. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

A cewar kwamishinan, yayin bincike mutanen ukun sun amsa cewa suna cikin kungiyar masu garkuwa da mutane, tare da bayyana sunayen wasu da ake zargin abokan aikinsu da suka hada da Sani, Dahiru, Lawali, Bello da Amadu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fara tone tone kan samun gawar budurwa a gidan ministan Tinubu

Ya ce kungiyar na kai hare-hare a kauyukan da ke cikin kananan hukumomin Tangaza, Gudu, Sabon Birni da Gwadabawa.

CP Shaffa ya jaddada cewa an gurfanar da dukkan wadanda ake zargi a gaban kotu, yayin da rundunar ke ci gaba da farautar sauran mambobin kungiyar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com