Lauya Abba Hikima Ya Samu Nasara da Ya Maka Hukumar FRSC Kara a Kotu
- Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke cewa FRSC ba ta da hurumin aiki a hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi
- Kotun ta ce tsayar da direbobi da jami'an FRSC suka yi a cikin birnin Kano ya saɓa wa kundin tsarin mulki
- Shari'ar dai an fara ta ne bayan lauya, Abba Hikima ya garzaya kotu don neman hakkinsa da ya ce jam'an hukumar FRSC sun take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ba ta da ikon gudanar da ayyukanta a kan hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi.
Kotun ta kuma bayyana cewa matakan da jami'an FRSC suka ɗauka a cikin birnin Kano ba bisa doka ba ne, kuma sun karya haƙƙoƙin jama'a.

Source: Facebook
Kotu ta soki ayyukan FRSC
Alkalin kotun, mai shari'a M.S Shuaiabu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026, rahoton jaridar Daily Trust ya nuna hakan.
Da yake yanke hukunci kan ƙarar da lauya a Kano, Abba Hikima, Esq., ya shigar a kan FRSC, Mai Shari'a M. S. Shuaibu ya ce jami'an hukumar sun wuce iyakokin ikon da doka ta ba su.
Kotun ta ce hakan ya faru ne lokacin da suka riƙa tsayar da direbobi, suna yi musu tambayoyi tare da jinkirta tafiyarsu a kan hanyoyin cikin gari a watan Yulin 2025.
Mai shari'ar ya bayyana cewa irin waɗannan matakai sun take haƙƙin 'yancin walwala da 'yancin zirga-zirga da sashe na 35 da na 41 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 suka tanada.
Umarnin da kotu ta bai wa FRSC
Kotun ta amince da duk manyan buƙatun da mai ƙarar ya gabatar, ciki har da bayar da umarnin hana jami'an FRSC ci gaba da tsayar ko takura wa direbobi a hanyoyin jihar Kano ba tare da halastacciyar doka ba.
Haka kuma, kotun ta umarci hukumar ta wallafa takardar neman afuwar jama'a a wata jaridar ƙasa, sannan ta biya mai ƙarar diyyar N800,000 da kuɗin shari'a.
Yadda aka fara shari'ar Abba Hikima
Rikicin ya samo asali ne a watan Yulin bara lokacin da jami'an FRSC suka kafa wuraren bincike a hanyoyin cikin birnin Kano, inda suka riƙa tsayar da direbobi, ciki har da Abba Hikima.
An ce jami'an sun riƙa neman lasisin tuƙi tare da yi wa direbobin tambayoyi ba tare da sun aikata wani laifin zirga-zirga ba.

Source: Original
Saboda haka Abba Hikima ya garzaya Babbar Kotun Tarayya domin ƙalubalantar abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa ba bisa ƙa'ida ba.
Lauyan ya kafa hujjar cewa ikon da dokar FRSC ta ba hukumar ya taƙaita ne ga manyan hanyoyin tarayya kaɗai, ba hanyoyin jiha ko na ƙananan hukumomi ba.
Kotu ta yi hukunci kan jadawalin INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun daukaka ta yanke hukunci kan karar da ta shafi jadawalin zaben 2027 da hukumar INEC ta fitar.
Kotun ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ya rushe jadawalin gudanar da zaben 2027 da hukumar zabe ta INEC ta fitar.
Asali: Legit.ng

