'Umarnin Boka ne': Makashin Fatima da Yaranta 6 Ya Fara Yi wa Kotun Kano Bayani

'Umarnin Boka ne': Makashin Fatima da Yaranta 6 Ya Fara Yi wa Kotun Kano Bayani

  • Umar, matashi da ake tuhuma da kashe kanwar mahaifinsa da 'ya'yanta shida a Kano ya shaida wa kotu cewa shi kaɗai ne ya aikata laifin
  • Umar Auwalu ya ce wani boka mai suna Thomas ne ya ba shi turare tare da umarnin ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuffuka
  • Ya kuma ce sauran mutane biyun da ake tuhuma ba su da hannu, ya bayyana dalilin da ya sa ambaci sunayensu bayan an kama shi da farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Babbar Kotun Jihar Kano ta ci gaba da sauraron shari'ar kisan Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida, inda babban wanda ake tuhuma, Umar Auwalu, ya bayyana wa kotu cewa shi kaɗai ne ya aikata kisan.

Kara karanta wannan

An kama mai ciki tana kai wa ƴan Boko Haram da ISWAP kayan aiki a Borno

Matashin mai shekara 23 ya yi wannan bayani ne yayin da yake kare kansa a gaban Mai Shari'a Nasiru Saminu a Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11.

An ci gaba da shari'ar Umar Auwal a Kano
Umar Auwal, wanda ake zargin dan uwa ne ga Fatima Abubakar da yagoranci kashe ta da 'ya'yanta 6 a Kano. Hoto: Hussaina Abkr
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa matashin ya bayyana wanda ya umarce shi da ya ci gaba da aikata irin wadannan laifuffuka na rashin imani da ya fara.

Kano: Dalilin Umar na kashe kanwar mahaifinsa

Umar ya shaida wa kotu cewa wani boka kuma mai sayar da maganin gargajiya mai suna Thomas ne ya ba shi wani turare tare da umartarsa ya aikata irin waɗannan laifuffuka kamar yadda ya ce ya taɓa yi a baya.

Ya kuma musanta zargin cewa Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu sun taimaka masa wajen aikata laifin kamar yadda aka yi tsammani tun farkon kama su.

A cewarsa, sunayen mutanen biyu sun shiga cikin binciken ne bayan ya ambace su sakamakon azabar da ya ce jami'an 'yan sanda sun yi masa bayan kama shi.

A zaman kotun na ranar Laraba 15 ga watan Yuli, 2026 lauyoyin gwamnati karkashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata sun gabatar da Kofural Aliyu Jamilu, jami'in dan sanda mai bincike, domin ba da shaida.

Kara karanta wannan

Sanata Hanga ya yi maganar amsa gayyata da APC ta nemi ya rabu da Kwankwaso

Haka kuma, lauyoyin masu kare wadanda ake tuhuma sun gabatar da shaidunsu a gaban kotun. Sannan an ɗage shari'ar zuwa 21 ga Yuli, 2026.

Kotu ta dage shari'ar Umar a Kano

n sauraron bangarorin biyu, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2026.

Ana zargin Umar Auwalu da kashe Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a gidansu da ke unguwar Dorayi Ciranci a ranar 17 ga watan Janairun 2026, lamarin da ya tayar da hankalin al'ummar Kano da ma Najeriya.

Umar ya ce shi ne ya kashe Fatima da yaranta
Taswirar jihar Kano inda aka kashe Fatima da yaranta Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayan binciken farko, 'yan sanda sun kama Umar tare da Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu, inda aka fara gurfanar da su a Kotun Majistare da ke Nomansland bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai, fashi da makami da kuma fyade.

Yayin da Umar ya amsa wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa, sauran mutane biyun sun musanta aikata wani laifi, kuma shari'ar na ci gaba da gudana a gaban kotu.

An kashe wata mata a Kano

A baya, mun wallafa cewa ana zargin wasu tsageru sun shiga har gida, sun kashe matar aure da dukkanin 'ya'yanta a unguwar Dorayi da ke cikin birnin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana tilasta wa ɗan jarida fallasa majiyoyinsa a shari'ar Ganduje

Wannan mummunan al'amari ya auku ne a unguwar Dorayi Chiranci, kuma an ce maharan sun jefa karamin jaririn matar a cikin rijiya inda ake zargin a ciki ya rasu.

Mazauna unguwar sun fito bayan an tabbatar da mutuwar mutanen, lamarin da ya daga hankulan dukkanin mutanen Kano da yankin Arewacin Najeriya a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng