Gwamna Abba Na Kano Ya Sake Faranta Ran Tsofaffin Ma’aikata da Biyan Kudin Giratutin N5bn

Gwamna Abba Na Kano Ya Sake Faranta Ran Tsofaffin Ma’aikata da Biyan Kudin Giratutin N5bn

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya dauka na ci gaba da biyan ‘yan fansho bashin da suke bin gwamnatin jihar Kano
  • A yau Laraba, 8 ga watan Mayu, Gwamna Abba Yusuf ya sanar da ba da umarnin kaddamar da biyan Naira biliyan biyar ga 'yan fansho a jihar
  • A cewar gwamnan, wannan zai zamo kashi na biyu na biyan kudaden bayan da ya biya Naira biliyan 6 a kashin farko a Disambar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Laraba ya amince da kashi na biyu na rabon kudin giratuti ga tsofaffin ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta shirin korar wadanda Ganduje ya dauka aiki

Abba Kabir na Kano ya kaddamar da biyan kudaden fansho a karo na biyu
Kano: Gwamna Abba Kabir ya sake cika wa 'yan fansho alkawarin da ya dauka. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

'Yan fanshon Kano za su samu N5bn

Akalla ma’aikata 6,000 da suka yi ritaya daga aikin gwamnati daga 2016 zuwa 2019 ne ake sa ran za su ci gajiyar N5bn da aka ware domin biyan su a kashi na biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake sanar da bayar da umarnin kaddamar da rabon kudin a shafinsa na X (Twitter), Gwamna Yusuf ya ce:

"Na amince da kaddamar da rabon kudaden giratuti ga ’yan fansho a jiharmu a karo na biyu.
"An ware Naira biliyan 5 domin rabawa tsofaffin ma'aikatan a wannan karon."

Abba ya rabawa 'yan fanshon Kano N6bn

A watan Disambarf 2023 ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon Naira biliyan shida ga 'yan fansho da iyalan ma'aikatan da suka mutu a jihar.

Da yake jawabi a taron fara rabon tallafin karo na farko wanda aka gudanar a gidan gwamnati, Gwamna Yusuf ya ce ya biya kudin ne duk da tarin kalubale da kuma rashin kudi a baitul mali.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kaddamar da titi mai hawa 3 a kan kudi ₦15bn a Dan Agundi

Ya ce gwamnatinsa ta damu matuka da halin da ‘yan fansho ke ciki musamman na kananan hukumomi domin su ne 'sha wuya' a matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Abba ya yi wa 'yan fansho alkawari

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alkawarin biyan ma'aikatan da suka yi ritaya daga shekarar 2016-2019 da kuma 2016-2020 bashin da suke bin jihar.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya dauki alkawarin biyan 'yan fansho da iyalan ma'aikatan da suka mutu wadannan kudi tun bayan da kotun daukaka kara ta tsige shi daga mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel