Gwamna Abba Na Kano Zai Faranta Ran Tsofaffin Ma’aikata, An Tsaida Ranar Fara Biyan Kudin Giratuti

Gwamna Abba Na Kano Zai Faranta Ran Tsofaffin Ma’aikata, An Tsaida Ranar Fara Biyan Kudin Giratuti

  • A karshen makon nan Abba Kabir Yusuf zai cika alkawarin da ya yi wa tsofaffin ma’aikata na biyansu kudin sallama
  • Ma’aikata da-dama sun yi ritaya daga aiki ba tare da gwamnati ta biya su kudin sallama na shekara da shekaru ba
  • Daga ranar Asabar Gwamnan jihar Kano za ta fara biyan miliyoyi ga wadanda hakkinsu bai wuce N2.5m zuwa N3m ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamnan jihar Kano za ta fara biyan giratutin ma’aikatan da su ka yi ritaya daga aiki kamar yadda ta dauki alkawari.

Daga ranar Asabar 2 ga watan Disamba 2023, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf za ta fara biyan kudin kamar yadda aka sanar.

Gwamna Abba
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sanarwa daga bakin Hadimin Gwamnan Kano

Kara karanta wannan

Ministoci 9 sun tashi da kaso mafi tsoka a kasafin kudin naira tiriliyan 27 da Tinubu ya gabatar

Mai taimakawa gwamnan a kafofin sadarwa na zamani, Abdullahi Ibrahim ya sanar da wannan a yammacin Alhamis a Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Kano za ta fara ne da manyan ma’aikatan da su ka yi ritaya daga aiki tsakanin 2016 da 2019.

Abdullahi Ibrahim ya ce wadanda za a soma biya hakkokinsu su ne wanda kudin sallamarsu bai wuce Naira miliyan uku ba.

Bayan su za a sallami wadanda su ka ajiye aiki daga shekarar 2016 da 2020 wanda kudin giratutinsu bai haura Nairamiliyan 2.5 ba.

Abba ya cika alkawarin da ya yi wa 'Yan Kano

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya dauki alkawarin zai biya wadannan kudi tun bayan da kotun daukaka kara ta tsige shi daga mulki.

Ma’aikatan da su ka rasu su na bin gwamnatin Kano bashin Naira miliyan uku zuwa kasa, duk suna cikin wadanda za a fara biya.

Kara karanta wannan

Kawu Sumaila: Sanatan NNPP Ya fede gaskiya a shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano

A dalilin haka aka bukaci wadanda su ka ajiye aikinsu a tsakanin wannan lokaci da su garzaya gidan gwamnati a ranar da za a fara.

Dama can an warewa 'yan fansho N6bn, yanzu ana bukatar duk tsohon ma’aikacin da zai je ya dauki takardun aikin da za a bukata.

Saboda haka ana kira ga tsofaffin ma’aikatan da su ka cancanta da su je gidan gwamnatin jihar Kano da karfe 9:00 na safiyar Asabar dauke da takardunsu domin a tantance su.

- Gwamnatin Kano

Shari'ar zaben Gwamnan Kano

Abba Yusuf ya daukaka kara da kotu ta tsige shi inda aka ji Alkalan kotun daukaka karan da su ka ba APC nasara a Kano sun yi katabora.

Majalisar NJC ta ce za a kafa kwamiti da zai yi bincike domin a dauki mataki a kan masu laifi a kotu saboda kura-kurai a takardun CTC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel