Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya da Bitcoin

Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya da Bitcoin

Bayan da Babban Bankin Najeriya ya sanar da cewa, zai fara gwajin wasu kudaden intanet da ya kirkira, jama'a na cike da tambayar yadda kudaden za su kasance, shin daya suke da Bitcoin da sauran tambayoyi. Mun kawo muku rahoton amsar tambyoyin nan.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa zai kaddamar da tsarin gwajin kudin intanet da aka yiwa lakabi da eNaira zuwa 1 ga Oktoba, 2021, The Cable ta ruwaito.

Rakiya Mohammed, daraktar fasahar bayanai na CBN, ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta kafar yanar gizo tare da masu ruwa da tsaki a ranar 22 ga Yuli.

Ta bayyana cewa babban bankin ya fara bincike kan kudin intanet na Babban Bankin (CBDC) tun cikin 2017.

A cewarta, an yiwa aikin suna da taken 'GIANT,' yayin da za a yi amfani da tsarin hada-hadar kudin intanet na Hyperledger Fabric Blockchain don aiwatar da aikin na eNaira.

Kara karanta wannan

Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000

Banbanci tsakanin kudin intanet da Najeriya ta kirkira da Bitcoin da kowa ya sani
Bitcoin | Hoto: nairametric.com
Asali: Getty Images

Takardar CBN da majiya ta samo ta amsa tambayoyin da suka dace game da kudin intanet na Najeriya da za a kaddamar nan ba da jimawa ba.

Menene CBDC?

CBDC wakilci ne na tsarin kudaden intanet masu cikakken iko da ake samar da su kamar yadda Babban Banki ke samar da kudi gama-gari.

Alhakin kai tsaye ne na Babban Banki ke samar dashi. Ba ana nufin maye gurbin tsabar kudi da tsarin ajiyar banki bane, ana nufin su yi aiki kunnen doki a matsayin karin nau'in hanyar biyan kudi da karba.

Shin daidai suke da kudaden intanet irinsu Bitcoin da Ethereum?

CBDC kai tsaye mallaki ne na Babban Banki kuma an samar da shi ne a hukumance. Hakan na nufin bankin koli zai iya amincewa ko soke ma'amala dashi tunda yana kula da abubuwan dake tafe tattare dashi sabanin sauran kudaden intanet.

Doka ce za ta amince da hulda da shi tare da cikakken iko.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Ya bambanta da sauran kudaden intanet masu zaman kansu. Doka bata amince da sauran kudade masu zaman kansu ba, kuma ba mallaki ne na wani Babban Banki ko wasu daga cikin cibiyoyin da aka kayyade ba.

Ba kamar nau'ikan sauran kudaden intanet ba da ke aiki ta hanyoyin sadarwa na blockchain ta hanyar da ba ta dace ba, CBDC mallakan kadari ne ta kasa da kuma kasar ke sarrafawa.

Ta yaya CBDC zai gudana?

CBN ta yi bayanin cewa tsarin eNaira CBDC ya hada da matakai 4 zuwa cikakken aiwatarwa da kuma tafiyarwa.

CBN ne ke da alhakin kerawa, kirkira da adana CBDC.

Za a rarraba CBDC ga cibiyoyin kudi da masu hada-hadar kudi masu lasisi wadanda za su ba da su ga mutane da sauran kasuwanni.

Cinikayya da CBDC na iya kasancewa akan yanar gizo ko akasin haka. Mutane da kamfanoni za su iya huldar kasuwa dashi nan take ta hanyar tashoshin biyan kudi na yanzu da na nan gaba (misali wayar hannu).

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

CBN za ta ci gaba da sa ido da kula da CBDC.

Gudummawar CBDC ga tattalin arzikin Najeriya

CBDC na iya rage farashin sarrafa tsabar kudi da 5%-7%, zai zurfafa hada-hadar kudi na intanet da habaka kasuwancin yanar gizo.

Zai inganta biyan kudade na kan iyaka cikin inganci, dacewa da araha.

CBDC zai kara zamanantar da tsabar kudi da habaka kasuwancin yanar gizo, gami da zurfafa hada-hadar kudi ta intanet.

Fa'idodin da zai iya samar wa ga gwamnati sun hada da samar da ingantacciyar hanyar da za a iya rarraba kudaden kasafi ga 'yan kasa.

Babban bankin ya kara da cewa eNaira zai rage kaucewa biyan haraji da kwararar kudaden haram. Ana kuma sa ran kudin zai inganta cinikayyar kan iyaka, inganta hada-hadar kudi, inganta aikawa da kudi, da sauran su.

Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro

A wani labarin, Firaministan Burtaniya, Boris Johnson, ya ce kasarsa a shirye take domin taimakawa Najeriya wajen yaki da matsalolin rashin tsaro da suka addabi kasar, BBC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya fitar, Boris Johnson ya ba shugaba Buhari tabbacin goyon bayan ne lokacin da ya gana da shugaba Buhari a gefen taron da ke gudana na habaka ilimi a Landan.

Shugabannin biyu sun kuma daddale cewa ya kamata a ba tsarin shari’a damar gudanar da ayyukanta bayan tantance yakin da ake yi da nau’ikan ta’addanci daban-daban a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel