Gwamnan Gombe Ya Fara Shirin Samawa Tinubu Kuri'a Miliyan 1 a 2027

Gwamnan Gombe Ya Fara Shirin Samawa Tinubu Kuri'a Miliyan 1 a 2027

  • Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da kwamitin sulhu na jam'iyyar APC mai mambobi 25 domin dinke baraka da kuma daidaita tsakanin 'yan jam'iyyar
  • Gwamnan ya bayyana cewa babban burin jam'iyyar shi ne ta lashe dukkan kujerun takara a jihar sannan ta samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri'u akalla miliyan 1
  • An daurawa kwamitin nauyin gudanar da aiki cikin gaskiya, adalci, da kuma kiyaye sirrin tattaunawa domin hana 'yan adawa damar amfani da sabanin da ke tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnan Jihar Gombe kuma jagoran jam’iyyar APC a jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da wani babban kwamitin sulhu na jam’iyyar mai mambobi 25.

An kafa kwamitin ne da nufin sasanta rikice-rikicen cikin gida, karfafa hadin kai, da kuma share fagen samun gagarumar nasara a babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ƴan sanda sun cafke mayakan Lakurawa da ke addabar garuruwan Arewa

Gwamnan jihar Gombe a wajen taro
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hadimin gwamnan ya wallafa a Facebook cewa ya ce Inuwa Yahaya ya bayyana cewa manufar APC a Gombe ita ce cin zabe da samawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuri'u miliyan 1.

Kira ga 'yan APC a Gombe

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kira ga dukkan mambobin jam'iyyar da ke jin an zalunce su a lokacin zaben fitar da gwani, da kuma zaben kananan hukumomi da aka yi kwanan nan, da su ajiye makamansu su rungumi tattaunawa.

Gwamnan ya bayyana cewa:

"Kamala ta Ubangiji ce kawai. A matsayinmu na bil'adama, ba za mu taba rasa kuskure a cikin harkokinmu na yau da kullum ba. Don haka,
"Ya zama dole mu fahimci cewa wasu shawarwari da sakamakon da aka samu daga wadannan zabuka na iya rashin yi wa wasu mambobinmu dadi, musamman wadanda suka nemi takara amma ba su yi nasara ba."

Ya kara da cewa kwamitin da mataimakin Gwamna, Dr. Manassah Daniel Jatau ke jagoranta, an kafa shi ne domin tattaunawa da dukkan 'yan jam'iyya da suka yi fushi domin dawo da amana, yafiya, da kuma karfafa hadin kan tafiyar APC.

Kara karanta wannan

Babban jigo a haɗakar su Atiku ya fice daga ADC, ya ɗora laifin kan El Rufai

Aikin da kwamitin APC zai yi

Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin adalci da gaskiya, tare da kiyaye sirrin duk abubuwan da aka tattauna yayin sulhun don kada abokan gaba na siyasa su yi amfani da hakan wajen raunana jam'iyyar.

Bayan haka, gwamnan ya ba kwamitin damar hada karfi da karfe da wasu mambobin idan bukatar hakan ta taso, da kuma rarraba ayyukansu zuwa yankunan jihar.

Ayyukan da aka dorawa kwamitin sun hada da:

  • Kasancewa tushen warware takaddama da samar da zaman lafiya na cikin gida.
  • Tattara dukkan korafe-korafen da suka taso daga ayyukan jam'iyya na baya-bayan nan.
  • Tattaunawa da daidaitawa tsakanin bangarorin da ke adawa da juna.
  • Tabbatar da cewa mambobin da aka sasanta sun yi tafiya kafada da kafada da manufofin APC da kuma tsarin cigaba na gwamnatin jihar.

Magana kan Muslim Muslim

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani jigon jam'iyyar APC, Farouk Aliyu ya bayyana cewa tikitin Muslim Muslim ba shi da matsala.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Kabir ya ba 'yan APC miliyoyi da filaye sama da 1,500 a Kano

Ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa kan neman jama'ar Najeriya su zabi shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Aliyu ya yi ikirarin cewa yanzu haka Kiristocin Najeriya ba su da wata matsala da Muslim Muslim lura da cewa bai cutar da su ba bayan samun mulki a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng