‘Ban Taba Neman Alfarma a Gare Ka ba’: Sanusi II Ya Fadi Buƙatarsu ga Abba Kabir
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yaba wa kokarin Gwamna Abba Kabir Yusuf da yake yi a fadin jihar ga al'umma
- Basaraken ya ji dadi kan ci gaban taron zikrin Tijjaniyya, yana cewa al'ada ce da sarakunan Kano na baya suka kafa
- Sarkin ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana cewa ya mara masa baya a zaɓen 2023 saboda ya yi imani da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fadi irin gudunmawar da suka ba Gwamna Abba Kabir a zaben shekarar 2023.
Sarkin ya yaba da ci gaba da gudanar da taron zikirin Tijjaniyya na shekara-shekara inda ya ce wannan kyakkyawar al'ada ce da sarakunan Kano na baya suka assasa.

Source: Facebook
Sanusi II ya bayyana haka ne yayin taron Tijjaniya na zikiri da ake yi duk shekara da aka gudanar a Kano kamar yadda Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook.
Tarihin al'adar zikirin Tijjaniya na shekara-shekara
Basaraken ya bayyana cewa marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, ya ci gaba da wannan al'ada bisa shawarar marigayi Sheikh Nasiru Kabara.
Tsohon gwamnan babban bankin CBN ya ce hakan ya taimaka wajen bunƙasa harkokin addinin Musulunci da inganta rayuarm mutane.
Sarkin ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin hidimar da yake yi wa al'ummar Kano, ya kuma tuna cewa ya fito fili ya mara masa baya.
Ya ce ya goyi bayan takarar gwamnan a zaɓen shekarar 2023 saboda ya yi imani da cancantarsa, ya ce malamai da dama sun yi hakan ne saboda yakini.
Sarkin ya ce bai taɓa zuwa wajen gwamnan domin neman wata alfarma ba. Ya ce bai taɓa neman kwangila ko muƙami ga ɗan kowa ba.

Source: Twitter
Abin da malamai ke bukata daga Abba Kabir
Sarkin ya ƙara da cewa malamai da suka mara wa gwamnan baya ma ba su taɓa neman wani abu na kashin kansu daga gwamnatin ba.
Sanusi II ya ce abin da suke buƙata kawai shi ne gwamnan ya nuna musu ƙauna kamar yadda su ke ƙaunarsa tare da yi masa addu'o'i.
Ya ce:
“Ban taɓa zuwa wajenka domin neman wata alfarma, kwangila ko naɗin muƙami ga ɗan kowa ba, haka kuma waɗannan malamai ba su taɓa neman irin waɗannan anfani daga gare ka ba, abin da kawai muke roƙo shi ne ka ƙaunace mu kamar yadda mu ma muke ƙaunar ka.”
Sarkin ya yaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin ke aiwatarwa a yankunan karkara da birane, ya ce da ba ya aiki da kyau, da bai yi shiru ba.
Ya bayyana cewa zai yi suka ga gwamnan idan bai gamsu da yadda yake gudanar da mulki ba, amma ya ce ayyukan da ake yi sun cancanci yabo.
Sanusi II ya fadi manyan matsalolin Arewa
An ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan aiwatar da ayyuka maimakon yawan sanarwar za su yi aiki.
Ya nuna damuwa kan yadda talauci, rashin ingantaccen ilimi da matsalolin kiwon lafiya ke ci gaba da addabar miliyoyin mutane a Arewa maso Yamma.
Sarkin ya bayyana haka ne a wani muhimmin zama da jagororin yankin suka yi a jihar Kano domin nemo mafita a kan matsalolin da suka dame su.
Asali: Legit.ng

