Kallo Ya Koma kan Najeriya, Tinubu zai Zauna Kusa da Trump a Amurka

Kallo Ya Koma kan Najeriya, Tinubu zai Zauna Kusa da Trump a Amurka

  • Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Bola Tinubu zai zauna kusa da Donald Trump a taron UNGA
  • Jimoh Ibrahim ya shaida wa manema labarai wannan bayan ganawa da shugaban kasa a Aso Villa a Abuja ranar Laraba
  • Tinubu yana shirin yi wa duniya jawabi kan ci gaban da gwamnatinsa ta samu tare da kara karfafa tsaro a iyakokin Yammacin Afirka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Najeriya za ta samu babban matsayi a zaman majalisar dinkin duniya na 81 (UNGA) da aka tsara a watan Satumban 2026.

Hakan ya zo ne bayan da jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron.

Bola Tinubu da Donald Trump
Bola Tinubu a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Jimoh Ibrahim ya fitar da wannan sanarwa ne yayin hira da manema labarai bayan da ya hadu da shugaba Tinubu a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

'Abin da ke saurin fusata Tinubu game da Buhari': Kashim Shettima ya magantu

Tinubu zai zauna da Trump

Jimoh Ibrahim ya ce Shugaba Tinubu zai zauna a kusa da shugaban Amurka Donald Trump a gaban dakin muhawara ta UNGA.

Ya kara da cewa ba zai iya tabbatar da ko za a gudanar da taro tsakanin shugabannin biyu ba, amma ya yi karin haske cewa hakan zai iya kasancewa.

"Na iya gaya muku a sarari cewa Shugaba Tinubu zai zauna kusa da Donald Trump a taron UNGA. Kada ku tambaye ni yadda aka shirya haka, amma hakan za ta faru,"

In ji jakadan

Dalilin zuwan Tinubu Amurka

A cewar Ibrahim, shugaban kasa yana shirin amfani da damar ne domin nuna wa kasashen duniya kokarin da gwamnatinsa ta samu tsawon shekaru uku da ta yi kan mulki.

Punch ta wallafa cewa Jimoh ya ce kuma an riga an tsara wa Tinubu wani jawabi da zai gabatar wa masu lura da siyasar duniya.

Bayan jawabi, za a samu tarurruka da Tinubu zai halarta, ciki har da batun samar da wutar lantarki da makamashi, ilimi da kuma bangaren lafiya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kare dangantakar majalisa da Tinubu, ya fadi dalili

Majalisar dinkin duniya
Zauren majalisar dinkin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Tsaron iyakokin kasashen Yammacin Afirka ma yana cikin abubuwan da za a yi magana a kansu a wajen taron.

Ya sanar da cewa shugaba Tinubu ya dauki nauyin kara karfafa hadin gwiwa da majalisar dinkin duniya domin duba halin iyakokin yankin Yammacin Afirka, musamman wajen yakar 'yan bindiga da masu ketare kan iyaka.

"Shugaban ya yi alkawarin hadin kai da majalisar wajen lura da iyakokin Yammacin Afirka.
"Za a yi kokarin kiyaye zaman lafiya. Na tabbata shugaban zai yi kokari sosai wajen tsaron iyakokin kasashen Yammacin Afirka."

Batun karar Tinubu wajen Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani kamfanin Amurka da ke da alaka da, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai kai karar Najeriya wajen Donald Trump.

Bayanin da kamfanin ya yi ya zo ne jim kadan bayan kama Ade Adeniyi Adeyemi da ake zargi da kafa ma'aikatar bogi a Najeriya.

Kamfanin ya sanar da cewa ya fara magana da jami'an gwamnatin Donald Trump da 'yan majalisar dokokin Amurka kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng