HoPE CT: Gwamnatin Tinubu Za Ta Bada Tallafin N180bn ga Talakawa Miliyan 3.6

HoPE CT: Gwamnatin Tinubu Za Ta Bada Tallafin N180bn ga Talakawa Miliyan 3.6

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin HoPE-CT ya isa ga fiye da iyalai miliyan tara domin rage radadin talauci
  • Ministan Yada Labarai, Idris Mohammed ya sanar da cewa za a bai wa iyalai miliyan uku da 600,000 tallafin N50,000
  • A hannu daya, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce za a bada lamuni marar ruwa har N400,000 ga mata da matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ƙarfafa aniyarta ta tabbatar da shirin "Renewed Hope" ta hanyar ƙaddamar da gagarumin shirin nan na bada tallafin kudi ga gidaje, watau HoPE-CT.

Ministan yaɗa labara, Mohammed Idris, wanda ya samu wakilcin Dr. Suleiman Haruna, ya bayyana wannan shiri a matsayin ɗaya daga cikin mafi tasiri wajen yaƙi da talauci a tarihin Najeriya.

Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da sabon shirin bada tallafin kudi ga 'yan Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na rattaba hannu kan wasu takardu. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Gwamnatin Najeriya za ta bada tallafin kudi

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda yakin Iran da Amurka ya shafi tattalin arziki da tsaron Najeriya

A cewar Ministan, wannan shiri ya riga ya isa ga mazauna ƙasar sama da miliyan 9.2, kuma ana sa ran zai taɓa gidaje miliyan 15 a faɗin ƙasar nan nan ba da daɗewa ba, in ji rahoton Vanguard.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati ta ware tallafi na musamman na N50,000 ga iyalai miliyan 3.6 waɗanda ke cikin mawuyacin hali domin rage masu raɗadin tattalin arziƙi.

Gwamnati ta jinjina wa ma'aikatar jinkai da rage radadin talauci bisa jajircewar da take nuna wa wajen gano ainihin mutanen da suka cancanci samun wannan tallafi a lungu da saƙo yau.

Lamuni mara ruwa ga mata da matasa

Baya ga tallafin HoPE-CT, gwamnati ta sake tsara fasalin shirye-shiryen tallafawa al'umma inda za a rinka bayar da lamunin kuɗi tsakanin ₦300,000 zuwa ₦400,000 ga mata da matasa.

Wannan lamuni ba shi da ruwa kuma ba ya buƙatar jingina, muddin za a bi ta hanyar ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin haɓaka sana'o'in dogaro da kai, in ji rahoton Radio Nigeria.

Haka kuma, hukumar gudanar da shirin tallafin ɗalibai ta riga ya amince da fitar da Naira biliyan 95.6 domin tallafawa ɗaliban manyan makarantu a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Hadimin Buhari ya rabu da APC, ya koma jam'iyyar hamayya a Kano

Ministan yada labarai ya ce gwamnati ta kuma shirya tallafawa mata da matasa da bashin N400,000 marar ruwa.
Ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris yana jawabi ga 'yan jarida. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Shirye-shiryen bunkasa fasaha da sana'o'i

Gwamnatin ta bayyana sauran shirye-shirye kamar 3 Million Technical Talent (3MTT) dake koya wa 'yan Najeriya miliyan 3 dabarun kimiyya da fasahar zamani.

Akwai kuma shirin Skill-Up Artisans (SUPA) wanda ke mayar da hankali wajen inganta dabarun ƙwararrun ma'aikata ta hanyar amfani da na'urorin zamani da fasaha.

Haka zalika, an sake farfaɗo da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu domin ƙarfafa yara su tafi makaranta da kuma tallafawa manoman yankunan karkara.

Ministan ya yi kira ga 'yan jarida da su mayar da hankali wajen bayar da rahotannin da ke nuna yadda rayuwar mutane take sauyawa sakamakon waɗannan tsare-tsare na gwamnati.

Amina Lawal Mailafiya ta shaida wa Legit Hausa cewa wannan yunkuri na gwamnati abin a yaba ne, la'akari da cewa 'yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.

"Idan har sun cika alkawarinsu, to sun yi abin a yaba. Gaba daya kasar ta rikice ne, kowa ka gani yana bukatar taimakon nan, ba magidantan ba, har da ma marasa aure.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano ɗan takarar shugaban ƙasa da PDP za ta marawa baya a 2027

"Babbar matsalar ita ce rashin gaskiya da za a sanya a wajen aiwatar da shirin. Sau tari za ka ji labarai ana an bada irin wannan tallafin, amma sai ka rasa su wa ake ba."

- Amina Lawal.

Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali sosai wajen ba matasa horon sana'o'in dogaro da kai tare da hada masu da jari idan sun kammala, kuma a rika bibiyarsu don tabbatar da cewa sun yi abin da ya dace.

An fara rajistar bada horo ga matasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta ƙaddamar da shirin yi wa ‘yan Najeriya rajista domin ba su horo kyauta a fadin ƙasar nan.

Wannan gagarumin shiri, wanda ke da nufin ilimantar da mutane miliyan 10 kan tsarin hada-hadar kuɗi da dogaro da kai, na ɗaya daga cikin manyan ayyukan Shugaba Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da fara rajistar shirin a ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2026, da nufin sauya rayuwar ‘yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com