Rana Ta Baci: Ƴan Bindiga Sun Yi Arba da Ƴan Sanda bayan Sun Sace Mutane a Sokoto

Rana Ta Baci: Ƴan Bindiga Sun Yi Arba da Ƴan Sanda bayan Sun Sace Mutane a Sokoto

  • Rundunar 'yan sandan Sokoto ta ce ta kwato dabbobi 689 daga hannun barayin shanu bayan ta dakile hare-haren 'yan bindiga a garuruwa daban-daban
  • 'Yan sanda tare da sauran jami'an tsaro sun kubutar da mutum takwas da aka yi garkuwa da su a Rabah da Binji bayan musayar wuta da 'yan bindiga
  • Kwamishinan 'yan sandan Sokoto ya ce rundunar na kara daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da dakile aikata laifuka a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yi da 'yan bindiga, masu satar shanu da sauran masu aikata manyan laifuka a fadin jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Hayatu Hassan Shaffa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar 16 ga watan Yuli, 2026, inda ya yi karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu daga watan Mayu zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana tilasta wa ɗan jarida fallasa majiyoyinsa a shari'ar Ganduje

'Yan sanda sun yi arangama da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Sokoto
Tawagar kwamishinan 'yan sandan Nasarawa a hanyar ruwa garin da aka kashe mutane fiye da 10. Hoto: @NigeriaStories
Source: Twitter

'Yan sanda sun kwato dabbobi 689

A taron, wanda wakilin mu ya halarta, kwamishinan ya ce rundunar ta kuma ci gaba da aiwatar da matakan tsaro da suka hada da sa ido kan motocin da ke karya dokokin hanya da kuma sauran shirye-shiryen hana aikata laifuka.

"Daga watan Yuni zuwa Yulin 2026, rundunar 'yan sandan Sokoto ta samu nasarori a wasu ayyuka da ta gudanar, ciki har da nasarar kwato dabbobi 689 da aka sace yayin da ta dakile hare-haren 'yan bindiga a sassa daban-daban na jihar.
"Jami'an rundunar tare da tawagar sauran jami'an tsaro sun yi musayar wuta da 'yan bindigar a lokuta daban-daban, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin dazuka.
"An gudanar da wadannan samame a kananan hukumomin Tangaza, Wamakko, Tureta, Bodinga da sauran yankuna, inda aka kama wasu da ake zargi tare da mayar da dabbobin da aka kwato ga masu su."

- CP Hayatu Hassan Shaffa.

Kara karanta wannan

Magidanci ya hau matarsa da duka kan abinci, Allah yayi mata rasuwa a Nasarawa

An kubutar da mutum 6 da aka sace

Kwamishinan ya ce a ranar 7 ga watan Mayu, 2026, 'yan bindiga sun tare hanyar Rabah zuwa Maikujera, inda suka bude wuta tare da yin garkuwa da mutum shida da ke cikin wata mota kirar Canter dauke da gawayi.

Ya ce:

"Bayan samun rahoton lamarin, jami'an 'yan sanda karkashin jagorancin DPO na Rabah tare da sojojin FOB sun garzaya wurin, inda suka fafata da 'yan bindigar.
"A sakamakon musayar wutar, 'yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji, yayin da aka kubutar da dukkan mutanen shida ba tare da sun ji rauni ba, tare da kwato motarsu kafin daga bisani aka mika su ga iyalansu."
'Yan sandan Sokoto sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su
Kwamishinan 'yan sandan Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa yayin magana da 'yan jarida. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

An ceto wasu mutum 2 a Binji

Hakazalika, CP Shaffa ya ce a ranar 20 ga watan Mayu, 2026, wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Jaredi da ke karamar hukumar Binji, inda suka yi garkuwa da mutum biyu.

Ya ce bayan samun kiran gaggawa, DPO na Binji ya hada kai da tawagogin musamman da sojoji domin bin sahun maharan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara bayan kashe manyan yan ta'adda 8 a Katsina

Bayan fafatawa mai zafi, jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar 'yan bindigar, suka kubutar da mutanen biyu, wadanda daga bisani aka hada su da iyalansu.

Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar 'yan sandan Sokoto za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin dakile ayyukan 'yan bindiga, kare rayuka da dukiyoyin jama'a, da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Gwamnan Sokoto ya tallafawa 'yan sanda

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Sokoto ta raba motocin sulke 62 da kayan aikin tsaro na sama da Naira biliyan 27 ga hukumomin tsaro a jihar.

Gwamna Ahmad Aliyu ya ce an yi haka ne a karkashin shirin Operation Fight Terrorism da nufin magance ta'addancin 'yan bindiga.

Ministan tsaro Christopher Musa ya halarci bikin, ya kuma yi kira ga sojoji da 'yan sanda su kasance a fadake wajen yakar 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com