Kotu Ta Hana Tilasta wa Ɗan Jarida Fallasa Majiyoyinsa a Shari'ar Ganduje

Kotu Ta Hana Tilasta wa Ɗan Jarida Fallasa Majiyoyinsa a Shari'ar Ganduje

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin game da shari'ar da ke neman a fallasa wanda ya yi tonon silili a shari'ar Abdullahi Umar Ganduje
  • Wannan ya zo bayan an samu bayanai da ake ganin na sirri ne game da danganta tsohon gwamnan jhar Kano da badakala game da tashar tsandauri
  • An matsala lamba domin tilasta wa 'dan jaridan da ya yi rahoton Abubakar Maishanu, da ya bayyana mutanen da suka ba shi bayanan bincikensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin cewa cewa kotu na da ikon gayyatar ɗan jarida domin ba da shaida a kan shari'a kan zargin Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai ya jaddada cewa har yanzu yana da haƙƙin kare sirrin majiyoyinsa, matuƙar ba a tabbatar cewa suna da alaƙa kai tsaye da shari'ar da ake saurare ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta mutumin da aka kama da laifin ta'addanci

Kotu ta hana a tilasta wa dan jarida sanar da sunayen da suka bankada a rahoto kan Ganduje
Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje/gudumar kotu Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: UGC

Jaridar Premium Times da ta wallafa labarin da ake shari'a a kai ta wallafa cewa Simon Amobeda ne ya bayyana hakan yayin zaman shari'ar da aka ci gaba da yi ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026.

Wannan ya zo ne bayan muhawara mai zafi tsakanin lauyan masu gabatar da ƙara, S.O. Ekwe, da lauyan wanda ake kara, Abubakar Mahmoud (SAN).

Dalilin fara shari'a da ya jawo 'dan jarida

Daily Post ta wallafa cewa shari'ar ta samo asali ne daga ƙarar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya shigar a kan Ahmad Rabiu, bayan wani rahoton bincike da jaridar Premium Times ta wallafa kan mallakar kamfanin tsandauri na Dala.

A zaman kotun, masu gabatar da ƙara sun nemi a kira ɗan jaridar da ya saki labarin, Abubakar Maishanu, domin ya ba da shaida.

Maishanu shi ne ya rubuta rahoton binciken da aka wallafa a watan Satumban bara, wanda ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauya mallakar 20% na gwamnatin jihar a tashar ga wasu mutane.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi ya yi magana a Kotu

Rahoton ya kuma yi zargin cewa wannan sauyin ya sanya 'ya'yan Ganduje suka zama masu hannun jari a kamfanin kafin gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar sama da N4 biliyan domin gina kayayyakin more rayuwa a tashar.

Haka kuma, rahoton ya ce sauyin ya kawo ƙarshen hannun jarin gwamnatin Kano a aikin, yayin da 'ya'yan Ganduje da mataimakinsa, Abubakar Bawuro, suka zama daraktoci da masu hannun jari.

Yadda dan jarida ya ba da shaida

Yayin da Maishanu ya hau mumbari domin ya bayar da shaida, ya tabbatar da cewa ya samo bayanan rahotonsa daga majiyoyi daban-daban.

Kotu ta ce dan jarida na da yancin kare majiyoyinsa
Tsohon shugaban APC Abdullahi Umar Ganduje a wani taron siyasa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Gnaduje OFR
Source: Twitter

Daga nan lauyan masu gabatar da ƙara ya nemi kotu ta tilasta masa bayyana waɗannan majiyoyi. Sai dai lauyan wanda ake kara, Abubakar Mahmoud (SAN), ya ƙi amincewa da wannan buƙata.

Abubakar Mahmoud (SAN) ya bayyana cewa doka na kare sirrin majiyoyin 'yan jarida, kamar yadda take kare sirrin hulɗar lauya da wanda yake karewa ko kuma bayanan marasa lafiya da likitoci ke da su.

Ya ƙara da cewa sai dai idan batun ya shafi barazanar tsaron ƙasa kai tsaye ne kawai za a iya yin la'akari da tilasta wa ɗan jarida bayyana majiyarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana dalilin da ya sa NIN ba ta gano masu garkuwa da mutane

Daga nan ne Alƙali Amobeda ya sallami ɗan jaridar tare da ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 15 ga Oktoba, 2026, domin ci gaba da shari'ar.

Dan jarida ya shiga hannu

A baya mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC a Najeriya ta bayyana cewa wani 'dan jarida, mai suna Alkazim Kabir ya shigo hannunta bisa zargin ya karya doka.

Hukumar ta sanar da cewa tana zarginsa same da hannu a harkokin damfara, karya da handame kudin jama'a da ya kai N14m ICPC ta hanyar amfani da dabaru daban-daban da suka hada da rancen makudan kudin kasar waje.

Binciken hukumar ICPC ya gano cewa Alkazim ya rika kwaikwayon hadiman Shugaban Kasa da Mataimakinsa, da kuma wasu 'yan Majalisar Tarayya domin damfarar bayin Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng