Sokoto: 'Yan bindiga sun sace shanu yayin da suka kai hari wurin kiwonsu kusa da filin jirgi

Sokoto: 'Yan bindiga sun sace shanu yayin da suka kai hari wurin kiwonsu kusa da filin jirgi

  • A kalla sama da shanu 200 sun yi layar zana yayin da barayin shanu suka kai hari wata gona da ke tsakanin Sakkwato da Bodinga, wacce bata fi kilomita 5 daga babban birnin jihar ba
  • Mai gonar ya kara da bayyana yadda barayin suka hada da tumakai da raguna masu tarin yawa da ya ke kiwatawa saboda cin kasuwar sallah a safiyar Talata
  • Sai dai daga bisani an ga wasu daga cikin dabbobin suna gararanba a wani daji da ke makwabtaka da su

Sokoto - 'Yan bindiga sun kai farmaki wurin kiwon shanu wanda ba shi da nisa da filin sauka da tashin jirgin saman Sultan Abubakar na jihar Sakkwoto.

Kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana, farmakin ya auku ne a safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi

Shanun Kiwo
Sokoto: 'Yan bindiga sun sace shanu yayin da suka kai hari wurin kiwonsu kusa da filin jirgi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gonar na tsakanin Sakkwato da Bodinga, nisan kilomita biyar daga babban birnin, Daily Trust ta ruwaito.

Ba a samu rahoton lamarin ya ritsa da kowa ba, amma mai gonar, Abdullahi S. Adiya ya bayyana yadda barayin suka yi awon gaba da fiye da shanu 200.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika, ya kara da bayyana yadda 'yan bindigan masu rike da mugayen makamai suka hada da tumakai da raguna masu tarin yawa.

Kamar yadda Adiya ya bayyana, ana shirya siyar da dabbobin ne yayin shagalin bikin babbar sallah.

"Na bar gonar jim kadan bayan tsakar dare zuwa gida, kawai aka kira ni da safen nan ana shaida min yadda barayi suka kai hari gonar gami da yin awon gaba da shanu da ragunan da muke shirin siyarwa."
"Na garzaya zuwa gonar amma bayanin da akwai na samu daga masu gadi shi ne yadda suke cikin shiri har karfe 3:00 dare, sai dai kawai suka gane yadda aka sace garkunan shanu daga gonar da safiyar nan," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Sai dai, daga bisani an ga wasu daga cikin dabbobin suna gararanba a dajin da ke kusa.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda jihar Sakkwoto, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce har yanzu ba a sanar dasu ba.

Zamfara: Sabon Farmaki ya Tilasta Mazauna Mada da Wasu Kauyuka Barin Gidajensu

A wani labari na daban, mazauna yankin Mada da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Gusau sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kai musu sabon farmaki.

Channels TV ta ruwaito cewa, Sabon harin 'yan bindigan da suka kai kwanan nan ya faru ne a ranar Alhamis, inda suka halaka wani 'dan sakai gami da garkuwa da kimanin mutane bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel