Mutane Sun Yi Kukan Kura Sun Kama Dan Bindiga a Jihar Kano

Mutane Sun Yi Kukan Kura Sun Kama Dan Bindiga a Jihar Kano

  • Rundunar 'yan sanda ta Kano ta sanar da kama wani mutum mai suna Mohammed Isah Haruna da ake zargi dan bindiga ne
  • Binciken da aka yi a jikin wanda aka kama ya nuna akwai harsashin AK-47, rigunan soji guda biyu da da wasu kayayyaki
  • Rahoton 'yan sanda ya ce wanda aka kama ya furta cewa ya zo ne domin kai kayan ga 'yan bindiga da ke boye a cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta sanar da kama wani mutum da ake zargi dan bindiga a karamar hukumar Bichi, inda aka same shi da kayayyaki da dama.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin, Mohammed Isah Haruna, mai shekaru 28 sanye da kayan sojoji.

Kara karanta wannan

Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya

Dan bindigan da aka kama a Kano
Dan bindigan da aka kama a hagu, kwamishinan 'yan sandan Kano a dama. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa wanda ake zargin ya fito ne daga karamar hukumar Dala, kuma an kama shi ne ranar Asabar bayan mazauna garin Rimaye sun ba jami'an tsaro bayanai kan halayyarsa.

An kama dan bindiga a Kano

Punch ta wallafa cewa mazaunan garin Rimaye sun ga wani namiji ya na saye da rigunan da ke kama da na sojan ƙasa, nan take suka sanar da jami'an tsaron yankin.

Jami'an sashen Bichi suka yi gaggawar tunkari zuwa wurin inda suka kama mutumin tare da taimakon al'ummar Rimawa.

Kiyawa ya ce:

"Al'ummar garin Rimaye, karamar hukumar Bichi, muna godiya. Sunyi kukan kura sun kamo dan bindiga."

Binciken da aka gudanar a jikin Haruna ya sa an same shi da abubuwa masu yawa waɗanda suka ƙara tabbatar da zargin da ake masa.

An samu jakar AK-47 wanda aka cika da harsasai 30, tare da wasu harsasai 79, rigunan soji guda biyu, hulunan soji guda uku da sauransu.

Kara karanta wannan

Bayan saukar Pantami a filin jirgi, gwamnatin Gombe ta yi barazanar bincike

Takalman soji da aka kama a Kano
Wasu daga cikin kayayyakin da aka samu wajen dan ta'addan. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Haka kuma an same shi da katin shaidar zama dan ƙasa na NIN, katin zaɓe da katunan ATM guda huɗu.

A lokacin tambayoyin da jami'an tsaro suka yi masa, Haruna ya amince da cewa ya je yankin ne da nufin isar da waɗannan kayan ga 'yan bindiga da ke ɓoye a cikin jeji.

Bayanin kwamishina 'yan sanda

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yabawa al'ummar Rimawa da gurin da suka nuna wajen sanar da jami'an tsaro.

"Wannan ya nuna muhimmancin haɗin gwiwar jama'a da rundunar 'yan sanda. Muna godiya ga al'ummar Rimawa da dukkan mutanen Kano. Tsaro nauyi a kan kowa,"

In ji Bakori.

Bayanin malaman da aka sace

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu daga cikin malaman da aka sace tare da dalibai a jihar Oyo sun yi magana.

Yayin da suke ganawa da Gwamna Seyi Makinde a Ibadan, shugabar makarantar ta bayyana irin wahalar da suka sha a daji.

Malamar ta bayyana cewa 'yan ta'addan sun lakadawa yara duka a lokacin da suke kuka saboda suna fargabar hakan zai sa a gano su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng