An gano gawar wani mutumi a gidan Mohammed El-Neny

An gano gawar wani mutumi a gidan Mohammed El-Neny

Jami’an tsaro sun kaddamar da bincike game da wata gawa da aka binciko a gidan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mohammad Elneny, don gano musababbin samun gawar a gidan, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gano gawar ne a wani sabon gida da Elneny ke ginawa a birnin Mahalla El Kubra na kasar Misra, don haka dan kwallon baya zama a gidan, amma mahaifinsa ne ya ci gano wannan gawa, kuma ya kai ma jami’an tsaro rahoto.

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun yi kira ga Buhari ya waiwayesu a kan nade naden mukamai

Mahaifin Mohammad, Naser Elneny ya bayyana cewa: “Da na Mohammed yana da gida a birnin Mahalla, kimanin nisan kilomita 123 daga binin Cairo, amma babu wanda ke zama a gidan.

“Na tafi gidan ne da nufin gudanar da wasu gyare gyare domin nan ne zamu mayar ofishin gidauniyar tallafi da Mohammed zai bude don amfanin jama’an Mahalla, kwatsam sai na ci karo da gawar mutum a tsaye yana rike da wayar wuta, nan da nan na kira Yansanda.

“Mohammed ya shiga damuwa, amma na tabbatar masa cewa babu komai, babu abinda zia faru, kuma magana ya kare.” Inji shi.

A yanzu haka Yansanda sun kama dukkanin abokan mamacin ta hanyar bin lambobinsu a cikin wayarsa, kuma sun gurfanar da wasunsu gaban kuliya manta sabo.

Shi kuwa Elneny ana sa ran zai koma kungiyarsa ta Arsenal don shirin fafatawa a sabuwar kakar gasar Firimiya ta bana, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar Misra inda ya buga wasanni 4 kacal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng