Bayan Ya Yi Bincike, Ɗan Majalisar Amurka Ya Gano Wadande ke Kashe Kiristoci a Najeriya

Bayan Ya Yi Bincike, Ɗan Majalisar Amurka Ya Gano Wadande ke Kashe Kiristoci a Najeriya

  • Dan Majalisar Dokokin Amurka, Riley Moore ya zargi Fulani da cewa su ne a kan gaba wajen kai hare-hare kan Kiristoci a Najeriya
  • Moore ya bukaci gwamnatin Amurka ta ƙara daukar mataki domin dakile kashe-kashe a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada cewa rikicin da kasar ke fama da shi ya samo asali ne daga rikici kan albarkatu da fadan addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Dan Majalisar Dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi zargin cewa Fulani masu dauke da makamai su ne suka fi kowa kai hare-hare kan Kiristoci a Najeriya.

Moore ya yi kira ga gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta sake daukar matakai domin dakile kashe-kashe a yankin Tsakiyar Najeriya.

Riley Moore.
Dan Majalisar dokokin Amurka, Riley Moore hana jawabi a taron manema labarai Hoto: @RileyMoore
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba, Moore ya ce ya dade yana gudanar da bincike kan abin da ya bayyana a matsayin kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca kaca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Ya ce:

"Tun lokacin da na fara bincike kan kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya, na gano cewa Fulani masu dauke da makamai ne suka fi kowa kai hare-hare kan Kiristoci."

Moore ya yabawa gwamnatin Trump

Ɗan majalisar ya kuma yabawa gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump, kan abin da ya kira manyan nasarori da aka samu wajen yaƙi da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Sai dai ya ce hakan bai isa ba, yana mai cewa:

"Dole ne mu dakatar da kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa ta Tsakiya ta hannun a1 idan muna son 'yan'uwanmu Kiristoci su rayu cikin aminci kuma su gudanar da ibadarsu ba tare da kashe su ba."

Yankin Middle Belt, wanda ya ƙunshi jihohi da dama a tsakiyar Najeriya, ya dade yana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.

Kalaman Moore na nuna yadda batun 'yancin addini da matsalar tsaro a Najeriya ke kara daukar hankali a Majalisar Dokokin Amurka.

Kara karanta wannan

An saki bidiyon bama baman da Putin ya harba babban birnin Ukraine

Bola Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin

Sai dai gwamnatin tarayya ta Najeriya ta sha bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Middle Belt ya samo asali ne daga matsalolin ta'addanci, fashi da makami da rikicin albarkatun kasa, ba wai saboda tsangwamar addini ba.

Haka kuma gwamnatin ta musanta ikirarin cewa ana aiwatar da kisan kare dangi ga mabiya wani addinina yankin, tana mai cewa babu wani abu mai kama da haka.

Amurka za ta bibiyi zaben Najeriya na 2027

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan Majalisar Wakilai na Amurka, Riley Moore ya ce gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta bibiyi harkokin zaben Najeriya na 2027.

Ya ce Amurka na ganin sahihin zaɓe a Najeriya muhimmin lamari ne, kuma za ta mai da hankali kan yadda aka gudanar da dukkan matakan zaɓen.

Moore ya kuma bayyana cewa Majalisar Wakilan Amurka na duba wani kudirin kasafi da ya ƙunshi tanade-tanade game da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262