Akwai Kallo: Amurka Za Ta Bibiyi Zabukan Najeriya da Za a Gudanar a 2027
- Wani ɗan majalisar Amurka ya ce gwamnatin Donald Trump za ta sa ido sosai kan yadda zaɓen Najeriya na 2027
- Riley Moore ya ce Majalisar Wakilan Amurka na nazarin kudirin doka da ya shafi Najeriya, musamman batun 'yancin addini da tallafin tsaro
- Kudirin ya tanadi ƙarin sharudda kan taimakon Amurka ga Najeriya, tare da buƙatar ɗaukar matakai kan rikicin addini da kare al'ummomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Amurka ta bayyana cewa za ta sa ido sosai kan yadda zaɓen Najeriya na shekarar 2027 zai gudana.
Ɗan Majalisar Wakilai Riley Moore ya ce gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta bibiyi sakamakon zaɓen da yadda aka gudanar da shi.

Source: Twitter
Moore, mai wakiltar jihar Yammacin Virginia, ya bayyana haka ne yayin wata hira da yan jarida wanda Punch ta bibiya.
Martanin Amurka kan zaben Najeriya a 2027
Ya ce Amurka na ganin sahihin zaɓe a Najeriya muhimmin lamari ne, kuma za ta mai da hankali kan yadda aka gudanar da dukkan matakan zaɓen.
Ya kuma bayyana cewa Majalisar Wakilan Amurka na duba wani kudirin kasafi da ya ƙunshi tanade-tanade game da Najeriya.
Kudirin ya shafi 'yancin addini, da kuma sharuddan bayar da tallafin tsaro daga Amurka.
Moore ya ce shi ma yana goyon bayan kudirin dokar da Chris Smith ya gabatar kan 'yancin addini da ɗaukar matakan hukunta masu take hakki a Najeriya, ya ce kudirin ya ƙunshi tsauraran sharudda kan alaƙar ƙasashen biyu.
A cewarsa, kudirin zai buƙaci ministan Harkokin Wajen Amurka ya riƙa gabatar da rahotanni ga Majalisa kan yadda ake magance muzgunawa mabambantan addinai da sauran manyan laifuka a Najeriya.
Ya ce kudirin zai kuma duba ko Najeriya na bin ƙa'idojin ƙasa da ƙasa kan 'yancin addini, yadda ake amfani da tallafin tsaro, takunkumai, agajin jin kai da matakan kare al'ummomin da ke cikin haɗari.

Source: Getty Images
Himmatuwar Amurka kan taimaka wa Najeriya
Moore ya bayyana cewa zai ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Trump kan batutuwan da suka shafi Najeriya.
Ya ce yana da shirin ganawa da Shugaba Trump domin ci gaba da tattauna waɗannan batutuwa masu muhimmanci, cewar Daily Pos.
Rahotanni sun nuna cewa Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilan Amurka ya riga ya amince da wasu tanade-tanade da suka ƙara tsaurara sharuddan tallafin kuɗi ga Najeriya a cikin shekarar 2026.
Kudirin ya tanadi cewa za a riƙe rabin kuɗaɗen tallafin da aka ware wa Najeriya har sai an tabbatar gwamnati na ɗaukar ingantattun matakai wajen dakile rikicin addini a faɗin ƙasar.
Majalisar Amurka ta karrama Gwamna Uzodinma
An ji cewa Majalisar Wakilai ta Amurka ta karrama Gwamna Hope Uzodimma da lambar yabo saboda kyakkyawan shugabancin da yake yi a Imo.
Wannan karramawa na zuwa ne yayin da Gwamna Uzodinma ke shirin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dattawan Birtaniya.
Majalisar ta yaba da ayyukan da gwamnan Imo ya aiwatar a fannin ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

