'Rai bai fi Rai ba': Bulama Ya Nemi Tinubu Ya Ceto Daliban Arewa a Hannun Yan Bindiga
- Masanin tsaro a Najeriya kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti ya yaba da dabarun da aka yi amfani da su a ceto daliban Oyo
- Ya bayyana cewa wannan ya kara haska bukatar da ake da shi a kan wasu dalibai a Arewacin Najeriya da aka sace a lokaci guda da na jihar Oyo
- Barista Bulama Bukarti ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba domin tabbatar da cewa daliban sun kubuta daga hannun yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuha – Masanin harkokin tsaro, Barista Bulama Bukarti, ya yabawa gwamnatin Tarayya bisa nasarar da ta samu wajen ceto ɗalibai da malamansu da aka sace a jihar Oyo.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka kutsa dajin Oyo, suka gwabza da 'yan bindiga yayin ceto dalibai
Sai dai yana ganin bai kamata a manta da wasu daga cikin mutanen Arewa da har yanzu suke tsare a hannun 'yan bindiga ba.

Source: Facebook
A hira da ya yi da DCL English, Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa ya kamata a ƙara matsa wa gwamnatin Tarayya lamba domin ta ɗauki irin matakin da ta ɗauka a Oyo wajen ceto sauran waɗanda aka sace.
Bulama Bukatarci ya magantu kan daliban Arewa
A kalaman Barista Blama Bukarti da ke fafutukar kare hakkin dan adam, kamata ya yi a yi amfani da dabarun ceto daliban jihar Oyo domin ceto na Arewa da aka yi garkuwa da su.
Ya ce:
"Manufata ita ce in matsa wa gwamnatin Tarayya lamba. 'Yan siyasa suna ɗaukar mataki ne idan al'amari ya zama abin da jama'a ke yawan tattaunawa."

Source: Facebook
A cewarsa, aikin ceton ɗaliban Oyo ya samu nasara ne saboda ingantaccen shiri da bayanan sirri da jami'an tsaro suka tattara kafin kai farmaki sansanin masu garkuwar.
Ya ce bayanan da ake da su sun nuna cewa an kashe kusan 'yan bindiga tara, an kama takwas, kuma babu ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto da ya mutu ko ya ji rauni yayin aikin.
Bulama Bukarti ya ce wannan ya nuna irin hanyar da ya kamata jami'an tsaro su bi wajen gudanar da irin waɗannan ayyuka.
Bulama ya jero daliban da aka sace
Barista Bulama Bukarti ya ce a ranar da aka sace ɗaliban Oyo, an kuma sace yara 42 maza da mata a ƙauyen Musa da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Ya ce har yanzu ba a san inda yaran suke ba, kuma ba a kuɓutar da su ba. Haka kuma kwanaki kusan 11 da suka gabata, an sace ɗalibai 36 da ke rubuta jarabawar NECO a garin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a Borno.
A cewarsa, ɗaliban sun haɗa da mata 25 da maza 11 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19, kuma an sace su ne suna cikin jarabawa.
Bulama Bukarti ya kuma ambaci mutanen Goshe, waɗanda ya ce suna da yawa, inda wasu rahotanni ke hasashen sun kai kusan mutum 400, duk da cewa bai tabbatar da adadin ba.
Bulama Bukarti ya yi magana kan Amurka

Kara karanta wannan
Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo
A baya, kun ji cewa fitaccen lauya, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana mamakin hango sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a cikin kudirin majalisar Amurka kan zargin kisan kiristoci.
Riley Moore, 'dan majalisar Amurka da ke kan gana wajen zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya ya ce sun gabatar da kuduri a gaban zaurensu domin duba a kan zargin muzgunawa kiristoci.
A cikin kudurin, an nemi Amurka ta hukunta wasu fitattun Najeriya da suka hada da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kungiyoyin Fulani Makiyaya da ake zargi suna kan gaba a zargin.
Asali: Legit.ng
