Kwankwaso Ya Aika da Sakon Ta'aziyya kan Rasuwar 'Ya'yan Tsohon Mataimakin Gwamna

Kwankwaso Ya Aika da Sakon Ta'aziyya kan Rasuwar 'Ya'yan Tsohon Mataimakin Gwamna

  • Allah ya yi wa wasu 'ya'ya biyu na tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, sakamakon hatsarin mota
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan wannan babban rashi da aka yi
  • Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa rashin da aka yi ya jawo bakin ciki a Masarautar Katagum da daukacin jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya mika ta'aziyyarsa ga tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela.

Kwankwaso ya aika da sakon ta'aziyyar ne bisa rasuwar yayansa biyu, Mustapha da Ummi, a wani mummunan hatsarin mota.

Kwankwaso ya yi ta'aziyyar rasuwar yaran Baba Tela
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya mika ta'aziyyar tasa ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin jagoran NDC na neman takaita tasirin Kwankwaso a Kano

Rabiu Kwankwaso ya yi wa Baba Tela ta'aziyya

Ya bayyana lamarin a matsayin wata babbar kaddara mai ban takaici da ta haifar da firgici da alhini mai yawa ba wai kawai ga gidan da aka yi rashin ba, har ma da Masarautar Katagum da ma daukacin jihar Bauchi.

“Ina mika ta'aziyya ta ga tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, bisa rashin yara da aka yi, Mustapha da Ummi, a wani mummunan hatsarin mota."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ce an yi rashi a Bauchi

Tsohon gwamnan ya ce wannan babban rashi ya sanya “bakin ciki a fadin Masarautar Katagum da ma daukacin jihar Bauchi.”

Ya yi wa iyalan da aka yi wa rashin addu'a tare da nuna alhininsa ga gwamnatin jihar Bauchi da al'ummar jihar.

“Tunanina da addu'o'ina suna tare da iyalan da aka yi wa rashi, gwamnati, da kuma mutanen kirki na jihar Bauchi a wannan lokaci mai wahala."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna kuma tsohon kwamishina a Bauchi ya riga mu gidan gaskiya

Kwankwaso ya mika sakon ta'aziyya
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Yadda suka bar duniya

Mustapha da Ummi sun rasu ne a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Bauchi zuwa Azare a ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026 yayin da suke dawowa daga Azare.

Biyo bayan wannan kaddara, gwamnan jihar Bauchi,Bala Mohammed ya mika ta'aziyyarsa ga Baba Tela, inda ya yi addu'ar Allah ya jikansu da rahama, sannan ya bukaci iyalan da aka yi wa rashin da su yi hakuri da kaddarar Allah.

Ya kuma nuna juyayinsa ga sauran wadanda suka samu raunuka a hatsarin tare da yi musu addu'ar samun sauki cikin gaggawa.

Tsohon kwamishina ya rasu a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yomi wa daya daga cikin tsofaffin kwamishinoni a jihar Gombe rasuwa

Tsohon kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Gombe, Hon. Ibrahim El-Hassan Kwami ya rigamu gidan gaskiya.

Marigayin wanda ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ya rasu ne ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026 a Gombe bayan ya yi fama da gajeruwar jinyar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng