Hukumar FAAN Ta Bayyana Gaskiya Kan Batun Siyo Motocin N200m Da Shugabanta Ya Yi

Hukumar FAAN Ta Bayyana Gaskiya Kan Batun Siyo Motocin N200m Da Shugabanta Ya Yi

  • FAAN ta musanta zargin da a ke yi cewa shugabanta ya siyo motar amfani a ofis wacce kuɗinta sun kai N200m
  • Hukumar ta bayyana cewa har yanzu sabon shugaban na ta baya da motar a yake amfani da ita a ofis
  • Hukumar ta yi nuni da cewa tsohon shugabanta ya bayar da kwangilar siyo motoci amma har yanzu ba a kawo ba

Hukumar kula da tashoshin jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta yi watsi da raɗe-raɗin cewa sabon shugabanta, Mr. Kabir Yusuf, ya kashe sama da N200m domin siyo sabuwar motar ofis.

An na ɗa Mohammed sabon shugaban hukumar FAAN ne a watan Mayun 2023, bayan shugaban ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari, ya cire shugaban hukumar na lokacin, Kyaftin Rabiu Yadudu, da wasu darektoci biyar na hukumar.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

FAAN ta karyata batun shugabanta ya kashe N200m
Hukumar FAAN ta bayyana cewa batun siyo motar N200m ba gaskiya ba ne Hoto: Medcars, FAAN
Asali: UGC

Idan za a iya tunawa dai wata kafar watsa labarai ta rahoto cewa Muhammad ya yi ta siyo abubuwan da ba su dace ba, yayin da filayen jiragen sama ke matuƙar buƙatar motocin sintiri bisa barazanar tsaron da su ke fuskanta a ƙasar nan.

A cewar kafar watsa labaran, an ware N200m domin siyo sabuwar mota ƙirar Toyota Land Cruiser, wacce Muhammad zai riƙa amfani da ita a ofis.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

FAAN ta ce shugabanta baya da motar ofis har yanzu

A cikin wata sanarwa da darektan hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Yakubu-Funtua, ya fitar, hukumar ta bayyana cewa tun lokacin da shugaban ya fara aiki, bar yanzu ba a ba shi mota ba, ko ya ware kuɗi ya siyo wa wani mota.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Batun cewa shugaban FAAN, ya fitar da N200m domin siyo mota ƙirar Toyota Land Cruiser domin amfanin kansa a matsayin motar ofis ƙarya ne. Tun lokacin da ya shiga ofis, shugaban FAAN ba ya da motar ofis kuma bai siyo wa wani mota ba."

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

A cewar rahoton The Sun, sanarwar ta bayyana cewa a lokacin da a ke raba tsofaffin motoci ga sabbin darektocin hukumar, an ba shugaban ɗaya daga cikinsu.

Sai dai, ya dawo da ita saboda motocin sun yi kaɗan a ce kowane daga cikinsu ya samu.

Peter Obi Ya Magantu Kan Hadewa Da PDP, NNPP

A wani labarin kuma, ɗan takarat shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya bayyana gaskiya kan batun dunƙulewa da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Ƙwankwaso.

Peter Obi ya bayyana cewa wannan batun jita-jita ce kawai wacce rabinta babun ƙamshin gaskiya a cikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel