Da Gaske Auren Laylah da Dan Majalisa Yusuf Gagdi Ya Mutu?

Da Gaske Auren Laylah da Dan Majalisa Yusuf Gagdi Ya Mutu?

  • Rahotanni sun nuna cewa dan majalisar tarayya, Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya musanta jita-jitar cewa ya saki matarsa, Laylah Ali Othman
  • A wani bayani da ya yi tare da iyalansa, dan majalisar ya bayyana cewa aurensu yana nan daram kuma soyayyarsa ga Layla ta ƙaru
  • Bugu da ƙari, Yusuf Gagdi ya wallafa bidiyon da aka dauka tare da matarsa a cikin gidansu domin nuna cewa jita-jitar ba gaskiya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan jita-jitar cewa ya saki matarsa, ɗan majalisar wakilai, Hon. Yusuf Gagdi, ya ce labarin ya rabu da Laylah Ali Othman ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana tare da matar a wani bidiyo yana tambayar wasu daga cikin 'ya'yan sa ko cewa da gaske ne ya saki Laylah domin nuna labarin ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Yusuf Adamu Gagdi da Laylah Othman
Dan majalisar wakilai, Yusuf Gagdi da matar shi. Hoto: Yusuf Adamu Gagdi
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Hon. Yusuf Gagdi ya yi ne a wani bidiyon da aka wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026.

Auren Laylah bai mutu ba

A bayanan da ya yi, dan majalisar ya bayyana cewa har yanzu yana tare da matarsa, Laylah, kuma soyayyar su kullum karuwa take.

Ya ce:

"An ce wai na saki matata da nake so, Dr. Laylah. Subhanallah! Gaskiyar magana ita ce, yanzu ne ma na fara ƙara fahimtar darajarta da kuma ƙaunarta fiye da da.
"Na wallafa wannan bidiyo ne domin waɗanda suke ta fatan aurenmu ya mutu su rungumi tiransifoma ko kuma su mutu da hawan jini.
"Da yardar Allah, gidanmu yana nan daram, kuma babu wata ƙarya ko mugun fata da za ta canja hakan. Ni da Laylah ba mu da lokacin baƙin ciki a zaman aurenmu... ku san haka ku huta."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya ya bukaci Tinubu ya dakatar da shirin sauya fasalin aikin NYSC

Ya yi addu'a da cewa:

"Allah Ya ci gaba da ƙarfafa aurenmu, Ya kuma ba kowane gida zaman lafiya. Amin"

Ra'ayoyin mutane kan batun

Muhammad Sharif ya yi magana cikin barkwanci yana cewa:

"Ina kan buzu na ina ja miki charbi Hauwa Kulu, Hon. ya shiga hannu, sai charbin nan ya tsinke. Ina tabbatar ya goya ki a baya kamar yadda kike goya marayu.
"Maza a turo fararen raguna rikon gida Maiduguri, a ci gaba da aiki."
Yusuf Adamu Gagdi da Laylah Othman
Yusuf Gagdi da Laylah Othman bayan sayen fon din takara. Hoto: Yusuf Adamu Gagdi
Source: Facebook

Hussaini Muhammad ya ce:

"Duk da yadda ka bayyana ƙaunarka ga matarka, mutane da dama sun lura cewa a cikin bidiyon tana ta duba wayarta, kamar ba ta ma lura kana kusa da ita ba.
"Ba furuci a kafafen sada zumunta ne kawai ke nuna soyayya ba, soyayya tana bayyana ne ta hanyar kulawa ta gaskiya, girmama juna, ba wa juna lokaci da kuma kyakkyawar mu'amala a sirrance.
'Idan aurenku yana cikin zaman lafiya kuma yana da ƙarfi, Allah Ya ci gaba da masa albarka. Amma mayar da martani ga jita-jita da zagi ko yi wa wasu fatan sharri ba ya ƙara wa saƙonka ƙarfi. Ya fi kyau kyawawan ɗabi'u, haƙuri da kuma yadda rayuwar aurenku take su yi magana a madadin ku"

Kara karanta wannan

Izala ta fadi halin da Sheikh Jingir ke ciki bayan yada cewa ba shi da lafiya

Muhammad Ibrahim Jalo ya ce:

"Subhanallah... bai kamata ka damu ba, tunda ita matarka ce kuma tana ƙarƙashin kulawarka. Domin gobe ma za su iya sake ƙirƙiro wani sabon labari."

Maganar auren Nafisat Abdullahi

A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban Hisbah a Kano, Mujahid Aminudden ya yi magana kan auren Nafisat Abdullahi.

Ya magantu yana mai cewa ya kamata a samu wani mutum mai hannu da shuni kuma mai nagarta ya auri jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan jarumar ta caccaki mata kan zaman aure da suke yi, inda ta ce suna zama bayin maza kuma ba za ta iya hakan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng