Masoyin Tinubu Ya Hango Matsala, Ya Magantu kan Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastam

Masoyin Tinubu Ya Hango Matsala, Ya Magantu kan Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastam

  • Wani mai goyon bayan Shugaba Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya ba da muhimman shawarwari gamea da hukumar Kwastam
  • Darazo ya ce ritayar manyan jami'ai lokaci guda na iya haifar da giɓin shugabanci da kawo cikas ga gyare-gyare da tara kuɗaɗen shiga
  • Ya kirayi ga Tinubu da ya tabbatar da ƙarin wa'adi domin tabbatar da ci gaba da kuma shirya sababbin shugabanni cikin tsari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Fitaccen mai goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manufofin Renewed Hope Agenda, ya ba da shawara ga gwamnatin tarayya.

Khamis Musa Darazo ya buƙaci shugaban ƙasa game da ƙara wa shugabannin Hukumar Kwastam ta Najeriya wa'adin aiki.

An shawarci Tinubu kan nada kara wa'adin shugaban Kwastam
Shugaba Bola Tinubu, Khamis Musa Darazo da shugaban Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Khamis Musa Darazo, Nigeria Custom Service.
Source: Facebook

Matashin wanda dan a mutun Tinubu ne ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa inda ya bayyana illar rashin tsawaita wa'adin shugabannin hukumar.

Kara karanta wannan

Kano: An gano abin da ya jawo mummunan arangama tsakanin manoma da makiyaya

Kalubalen da za a iya fuskanta a Kwastam

Ya ce kusan dukkan mambobin tawagar shugabancin hukumar za su yi ritaya kafin ƙarshen shekara, lamarin da ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke buƙatar matakin gaggawa daga shugaban ƙasa.

A cewarsa, ficewar manyan shugabannin lokaci guda na iya kawo cikas ga ci gaba da manufofi, gogewar hukuma, ingancin aiki da sauye-sauyen da suka inganta ayyukan kwastam da tara kuɗaɗen shiga.

Darazo ya ce Hukumar Kwastam tana da muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Najeriya, musamman yayin da gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da ba na mai ba.

Ya ce:

"Hukumar Kwastam ta Najeriya tana da muhimmiyar rawa a tsarin tattalin arzikin ƙasarmu. A wannan lokaci da Shugaba Tinubu ke aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki tare da ƙarfafa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga da ba na mai ba, ci gaba da riƙe gogaggun shugabanni a cikin hukumar yana da matuƙar muhimmanci domin dorewar nasarorin da aka samu."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya

Ya ƙara da cewa jami'an da ke jiran gado galibi mataimakan Kwanturolan Kwastam ne, waɗanda har yanzu ke buƙatar ƙarin gogewa kafin ɗaukar manyan nauyin shugabanci.

Ya kuma yi gargaɗin cewa giɓin shugabanci na iya buɗe ƙofa ga naɗin mutanen waje a muƙaman da jami'an kwastam masu aikin dindindin suka saba riƙewa, cewar Vanguard.

An ba Tinubu shawara kan tsawaita wa'adin shugaban Kwastam
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Rokon da Darazo ya yi ga Tinubu

Darazo ya roƙi Shugaba Tinubu da ya yi la'akari da ƙarin wa'adin aiki ga shugabannin hukumar a matsayin matakin wucin gadi domin tabbatar da ci gaba, kwanciyar hankali da sauyin shugabanci cikin tsari.

Ya ce hakan zai taimaka wajen kare muradun Hukumar Kwastam na dogon lokaci, ci gaba da gyare-gyare, ba da horo ga sababbin jami'ai da kuma ƙarfafa ayyukan tara kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Masoyin Tinubu ya saya masa ragon layya

A baya, an ji cewa wani matashi daga jihar Bauchi ya bai wa Shugaba Bola Tinubu ragon Sallah a matsayin godiya kan bayar da lasisin aikin mai na Kolmani.

Ya bayyana cewa wannan lasisi zai kawo ci gaban tattalin arziki da damammaki ga Arewacin Najeriya da ma kasa baki ɗaya.

Khamis Musa Darazo ya ce yana nuna ƙauna ta musamman ga Tinubu tun kafin ya hau mulki, har ya sa wa 'yarsa sunan mamar shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.